Rabe-Raben Abinci

Gabatarwa
An karkasa abinci zuwa rukuni-rukuni ko aji-aji (Groups or classes), bisa la'akari da sinadaran da kowannensu ke ɗauke da shi. Babban dalilin yin wannan shi ne samun sauƙi wajen ganewa tare kuma da rarrabe nau'ukan abincin don samun sauƙin mu'amala da su.
Masana wannan fanni na abinci sun bambanta dangane da yawan ajujuwan da suka karkasa abinci. Wasu sun tafi a kan cewa guda shida ne (Ojumu, 2016; Hernandez, 2016; Khosroshahi, 2009), sun kawo guda shida kamar haka: Kabohydirets (carbohydrates), bitamins (vitamins), furotins (proteins), minarals (minerals), ruwa (water) da kuma maiƙo (fats and oil).
Amma mutane kamar irin su dakta Amirul Islam (2010), da kuma ƙungiyar likitotci ta Medic8, sun ruwaito guda bakwai ne kamar haka: kabohaidirets (carbohydrates), faiba (fibre), maiƙo (fats), furotin (protein), minarals (minerals), bitamins (vitamins), da kuma ruwa (water).
Manazarta:
Amirul-Islam M. (2010). Carbohydrates, Proteins, Vitamins and Minerals. An ciro a shekarar 2016, daga shafin:http://wikieducator.org/
Hernandez A. (ba kwanan wata). 6 Essential Nutrients and Their Functions. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://healthyeating.sfgate.com/6-essential-nutrients-functions-4877.html
Khosroshahi H. (2009). The Six Classes of Nutrients and Their Functions. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://ezinearticles.com/?The-Six-Classes-of-Nutrients-and-Their-Functions&id=3333582
Medic8 (2016). The Food Groups. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.medic8.com/healthguide/articles/ foodgroups.html
Ojumu B. (2016). Classes of Food. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://passnownow.com/classwork-series-exercises-social-studies-jss2-classes-food/
Robbins C. (2015). Six Classes of Foods. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.livestrong.com/article/511440-6-classes-of-food/
Abinci
Ɗakin Karatu
Harshen Turanci
Jama'iyyun Siyasa
Kimiyyar Kwamfuta
.jpg)
Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin