Sarkin Dutse Abdulƙadir III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abduƙadir Ɗan Ibrahim 1901 – 1903


Gabatarwa

Sarki Abdulƙadir Ɗan Ibrahim Bayallige, shi ne sarki na talatin da takwas a jerin sarakunan Dutse, sannan kuma sarki na goma a jerin sarakunan Fulani a Dutse. Sarki Abdulƙadir Ɗan Musa shi ne Sarki na ƙarshe a jerin sarakunan da suka yi sarautar Dutse kafin zuwan Turawa. Shi mutum ne mai tarin ilimin addinin Musulunci wanda ya goge a fannin tauhidi.

Bayan rasuwar Sarkin Dutse Abduƙadir Ɗan Musa (1894 – 1901), sai Sarkin Kano Alu (1894 – 1903) ya naɗa Sarki Abdulƙadir Ɗan Ibrahim. Sai dai, zamaninsa bai yi tsawo ba.

A ranar 2 ga watan Janairu na shekarar 1903, Sarki Abdulƙadir Ɗan Ibrahim tare da tagawar Sarkin Kano Aliyu Ɗan Abdullahi (1894 - 1903), suka tafi ziyarar ban-girma zuwa ga Sarkin Musulmi Attahiru I, a fadarsa da ke sakkwato.

Bayan tafiyarsu da kamar sati huɗu, sai Turawa suka kawowa Kano hari, suka kuma ci ta da yaƙi, inda labari ya same su a kan hanyarsu ta dawowa Kano. Samun wannan labari ya saka shi Sarkin Kano Aliyu Ɗan Abdullahi (1894 – 1903), juyawa zuwa Sakkwato, amma bai kai can ba Turawa suka cim-masa, suka tursasa masa yin hijira zuwa Lokoja garin da a can rayuwarsa ta ƙare.

Shi kuwa Sarkin Dutse Abdulƙadir Ɗan Ibrahim, ya juya ne zuwa Sakkwato dan taimakawa Sarkin Musulmi Attahiru. Bayan da suka isa Sakkwato sai suka tarar da Sarkin Musulmi Attahiru yana shirin tafiya ƙasa mai tsarki (Makka) dan gudun hijira.

A ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1903, wannan tawaga ta sarkin Musulmi ta iso Kano a kan hanyarta ta zuwa Makka. Da isowarsu garin Kano, Sarkin Kano Muhammadu Abbas Ɗan Abdullahi (1903 – 1919), ya bayar da umarnin cewa kar kowa ya bi wannan tawaga. Amma duk da haka sai da aka samu mutane sama da ɗari bakwai daga Dutse da suka bi tawagar sarkinsu.

A ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 1903, Turawa suka farwa wannan tawaga a yunƙurinsu na kashe Sarkin Musulmi Attahiru a garin Burmi. A nan Sarkin Musulmi Attahiru da Sarkin Dutse Abduƙadir Ɗan Ibrahim tare da dubban mayaƙan Musulmi suka yi shahada.

Manazarta:


NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). Stories of Dutse Palace, 1421 - 2009. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.

Sanusi N.M. (2015). The Days in My Life. An buga a Maɗaba'ar Jahar Jigawa, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub