Me ka ke nema?


Shafin Farko

Manyan Haƙƙoƙin Ɗan’adam a Ghana


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sashe na 12: Kare Manyan Haƙƙoƙin Ɗan’adam da ‘Yanci

  1. Muhimman haƙƙoƙi da ‘yanci-‘yanci da aka ƙunshe a cikin wannan kashi su zama ababen girmamawa da kuma marawa baya da shugabanni, ‘yan majalisa da kuma fannin shari’a da dukkan sauran rassan gwamnati da hukumominta da kuma guraren da abin ya shafa, ga duk ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa da kuma rajista a Ghana, kuma ya zama abin zartarwa a kotuna kamar yadda wannan kundin tsarin mulkin ya tanada.
  2. Kowane mutum a Ghana, ko daga wace irin ƙabila ya fito, gurin haihuwa, ra’ayin siyasa, launin fata, addini, jinsi, ya cancanci muhimman haƙƙoƙi da kuma ‘yancin ɗaiɗaiku da ke ƙunshe cikin wannan kashi amma bisa dogaro da girmama haƙƙi da ‘yancin wasu da kuma buƙatun al’umma.

Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub