Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kariya Daga Ƙwacen Kadara Ghana


Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sashe na 20: Kariya Daga Ƙwacen Kadara

Wannan sashe ya zayyana waɗannan tanade-tanade a matsayin 'yancin duk wani ɗan Ƙasar Ghana ta fuskacin Kariya Daga Ƙwacen Kadara.

 1. Babu wata kadara ta kowacce irin fuska, ko ra’ayi a ciki ko haƙƙi a kan kowacce dukiya da bisa dole za a karɓe mallakarta ko a wata Jaha ta karɓe sai dai sharruɗa masu zuwa sun kammala:
  1. Karɓar mallaka ko samu ya zama dole a bisa buƙatar tsaro, kiyaye lafiyar al’umma, dokar gama-gari, kyautata halayen al’umma, lafiyar al’umma, tsara gari da ƙasa ko haɓɓakawa ko sarrafa kadara ta hanyar da za ta haɓɓaka amfanin al’umma; da
  2. Wajabcin karɓar an bayyana shi a fili wanda kuma shi ne a samar da gamsasshiyar hujjar da ta haifar da wani tsananin da zai iya kaiwa ga wani mutum wanda ke da ra’ayi a ciki ko haƙƙi a kan wannan kadara.
 2. Karɓar kadara bisa dole daga gwamnati zai faru ne kawai a ƙarƙashin dokar samar da gurabe domin:
  1. Aiwatar da biyan madadi da kuma wadatacciyar fansa; da
  2. ‘Yancin isuwa ga Babbar Kotu ga kowane mutum wanda yake da ra’ayi a ciki ko haƙƙi a kan kadara wanda ka iya zama kai tsaye ko kuma ta hanyar ɗaukaka ƙara daga kowacce hukuma ce daban domin neman ra’ayin nasa ko haƙƙi da kuma adadin fansar da ya cancanta.
 3. A yanayin da karɓa ko mallakar ƙasa don dole ya faru daga Gwamnati kuma bisa tanadi na (1) na wannan sashe ya haifar da sauyawa ‘yan asalin gurin matsugunni, Gwamnati ta sake tsugunnar da ‘yan asalin gurin a wata nagartacciyar Ƙasar tare da cikakkiyar kulawa ga abin da ya shafi ingancin tattalin arziƙinsu da walwala da al’adunsu.
 4. Babu wani abu a cikin wannan sashen da za a ɗauka cewa yana da tasiri wajen aiwatar da kowacce dokar gama-gari ya zuwa wannan gaɓar kamar yadda ta tanada domin mallaka ko karɓar kadara:
  1. Ta hanyar ɗorawa ko gudanar da (administration of) kadara ta gaskiya, kadarar maƙiyi ko kadarar mutanen da aka yankewa hukunci ko aka ayyana a matsayin bashin banki ko an gaza biyan bashi, mutane marasa lafiyayyiyar zuciya, mamaci, ko kamfanoni ko kuma marasa rijista a ƙoƙarin yi masa giɓi; ko
  2. A cikin aiwatar da hukunci ko umarnin wata kotu; ko
  3. Bisa dalilin zamowarta cikin yanayin hatsari ko mai illatar da lafiyar jama’a, dabbobi ko tsirrai; ko
  4. A cikin hunkuntawar kowacce doka tare da girmama iyakance ayyuka; ko
  5. Zuwa tsawon lokacin da zai iya zama dole bisa dalilin kowacce irin tantancewa, binciken ƙwaƙwaf, tuhuma a kotu ko tambayoyi; ko
  6. Zuwa tsawon lokacin da zai iya zama dole bisa dalilin gudanar da aiki a kan kowacce ƙasa domin samar da wasu ababe ko guraren amfanin jama’a, sai dai a guraren da kowacce irin ɓarna da ta faru biyo bayan irin wannan aikin sai a biya fansa bisa dacewa.
  7. Duk wata kadara da aka karaɓe mallakarta bisa dole ko aka mallaka domin buƙatar jama’a ko domin buƙatar hukuma a yi amfani da ita kawai domin wannan buƙatar ta jama’a ko kuma ta hukumar wadda aka karɓa dominta.
  8. A yanayin da ba a yi amfani da kadarar domin buƙatar jama’a ko ta hukuma ba wadda aka karɓa dominta, mamallakin kadarar dab da ƙwacen dole, a bashi zaɓin farko na mallakar kadarar kuma ya, game da wannan sake mallakar dawo da duka ko wani sashe na fansar da aka biya shi kamar yadda aka tanada bisa doka ko waɗansu adadi kamar yadda aka kimanta da darajar kadarar a lokacin karɓar kadarar.


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci
Haƙƙoƙi da ‘Yanci
‘Yancin Rayuwa
'Yancin Walwala
Girmama Ɗan'adam
Kariya Daga Bauta
Yancin Daidaito
Kaɗaikatar Gida
Adalcin Shari’a
Kariya Daga Ƙwace
Muhimman ‘Yanci

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub