Nii Adam Kwatei Quartey

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Nii Adam Kwatei QuarteyNii Adam Kwatei Quartey
Hoto:spyghana.com

Gabatarwa

Baya goya marayu! Rumfa sha shirgi! Shi ne kallon da dukkan zuriyar Gbawe suke yi wa jagoransu, Nii Alhaji Adam Kwatei Quarty. Mutum ne mai matuƙar son zaman lafiya da haɗin kan al’ummarsa, adalci, mai haƙuri, mai ƙasƙantar da kai, yadda da ƙaddara da kuma tsaya ƙyam, wajen ganin ya ƙwato wa al’ummarsa ‘yancinsu.

Allah Ya albarkace shi da cin babbar ribar rayuwa, “… Wallahi, Allah Ya shiryi koda mutum ɗaya ne ta hannunka ya fi maka alheri daga garken jajayen raƙuma” in ji Manzon Allah (SAW) kamar yadda ya zo a ƙarshen hadisi mai lamba 174 a cikin littafin Riyaadussaalihiin.

Allah Sarkin daɗi; Mai kyauta da ƙari. Shi Ya so ya bai wa Alhaji Adam ikon gina masallatai, maƙabartu, raba filayen gina gidaje, tallafa wa marasa shi da sauran abubuwan alherin kamar yadda Sarkin Musulmin dukkan masarautar, Alhaji Sheikh Lamiɗo, Mohammed Jibril Sissy ya labarta mana a cikin tattaunawarmu da shi. Wannan aiki kuma yana daga cikin sadakar da ladanta baya yankewa, wato sadaƙatuj-jariya.

Ta cikin wannan shafin muke fatan baka labarin wannan bawan Allah. Muna fata karatun ya zama manuni ga masu karatu domin koyi da shi.

Haihuwa

An haifi Alhaji Adam Kwatei Quartey a garin Gbawe da ke lardin Accra, a Ƙasar Ghana cikin shekarar 1923. Sunan mahaifinsa Nii Boye Quarte.

Karatu

Alhaji Adam Kwatei Quarte ya yi karantun fimarare na lokacin da ba mai tsawo ba; wato shekaru uku. Daga nan kuma Allah bai bayar da ikon cigaba ba.

Zamowarsa Sarki

Alhaji Adam Kwatei Quarte ya zama Nii Adam Kwate Quarte bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 1972 inda manyan wannan ƙabila tasu suka amince da naɗinsa a matsayin jagoran dukkan danginsu sannan kuma Dzaasetse na zuriyar Gbawe. Tun daga sannan yake jan zare har zuwa lokacin rubuta wannan tarihin nasa (2021).

Musuluntarsa

Ba jimawa da hawan Nii Adam wannan kujera ta shugabanci haɗi da sarauta, sai Allah Ya kawo malamai masu wa’azi daga yankin Mabrouk da ke cikin Unguwar NIMA a Accra da nufin isar da saƙon Allah ga mutanen wannan yanki.

Bayan Kwatei Quarte ya saurari wannan wa’azi, sai abin ya ratsa zuciyarsa. Nan take ya ɗaga hannu ya yi wa masu wa’azi tambaya da cewa, “Mutumin da mahaifansa suka zama ba Musulmai ba zai iya Musulunta?” kamar yadda ya bayyana mana a cikin tattaunawarmu da shi a gidansa da ke gundumar Gbawe, cikin Lardin… a Accra babban Birnin Qasar Ghana a ranar Litinin 23/8/2021. Sai suka amsa masa ta hanyar bashi ƙissar Annabi Ibrahim (AS) daga cikin Alƙur’ani Mai Girma da kuma Bayibul.

Tun daga wannan lokaci yake ta lallashin matarsa cewa su karɓi addinin Musulunci wadda ita kuma ta ce fir! Ta yi tsallen baɗake ta ƙeƙasa ƙasa cewa sai dai su koma cocin Katolika (Catholic Church), wato su zama Kiristoci kenan. Haka dai bawan Allah ya cigaba da lallaɓarta. Bata yarda ba sai bayan shekaru biyu suka karɓi Musulunci da shi da matarsa da ‘ya’yansa da kuma ƙarin wasu mutane uku da suma suka tuba daga baya.

Biyowa bayan wannan karɓar Musulunci da Alhaji Adam ya yi, sai ya kafa wani masallaci a fadarsa mai tubali uku, wanda daga aka gine shi. Wata rana sun yi sallar Magriba suna jiran su yi Isha’i, sai ga askarawan Ghana sun dira a gurin tare da tambayar ko wane ne Adam? Shi kuma ya ɗaga hannu ya ce da su gashi. Nan take suka tafi da shi babbar barikin sojojin Ƙasar Ghana; wato Gonja Barrack a Turance.

A kan hanyarsu ta tafiya, sai suka ce da shi, “Kai da ba Bahaushe ba me ya kai ka shiga Musulunci?” sai ya amsa musu da cewa: “Wa’azi aka zo aka yi shi kuma ya saurara ya gamsu”. Faɗin haka ke da wuya, sai wani daga cikinsu ya ɗauko bindiga ya rafka masa a ƙoƙon ka, da haka suka kai shi suna duka tare kuma da cigaba da wannan azabtarwa har tsawon sati uku.

Lokacin da yake tsare jama’a sun riƙa tururuwa suna kai masa ziyara. Sakamakon haka, sai aka gindaya masa sharaɗin cewa ya samo mutane biyu da za su yi belinsa shi kuma ya aikata haka inda ya kira ’yan’uwansa biyu; Ataa Laryea da Mohammed Laryea, wanda shi na biyun shi ne ya yi sanadiyyar zuwan waɗannan masu wa’azi wannan yankin na ƙasar Alhaji Adam, kasantuwar tun kafin wannan lokaci ya karɓi Musulunci sai ya yi sha’awar isar da shi ga ‘yan’uwansa wanda kuma ya yi bisa dace.

Daga ƙarshe aka sake shi tare da da sharaɗin cewa kullum da safe zai riƙa kai kansa Majalisar Ƙasa. Ya je yau, ya je gobe sai aka tambaye shi wa ya saka shi ya riƙa zuwa? Sai ya amsa da cewa sojoji ne. Aka sake tambayarsa cewa ina takardar da aka bashi ya ce ba a bashi takarda ba, “Sai aka ce da ni na tafi. To tun daga wancan lokaci har zuwa yau ban sake jin komai ba”, a ta bakin Dattijjo Alhaji Adam Kwatei Quarty a yayin zantawarmu da shi.

Mai magana da yawun dukkan zuriyar Gbawe ya siffata Nii Adam Kwatei Quarty da mutum mai “Fara’a, maraba da kowa, saukin kai, mai yawan kyauta, mai ƙarfafa guiwa, mai bayar da shawara, a sama da komai kuma dukkan rayuwarsa abar koyi ce”.

Wannan shi ne Nii Alhaji Adam Kwatei Quarty, shugaba kuma jagoran zuri’ar Gbawe, amma fa a taƙaice.

Manazarta:

Ghanaina Democrat (2019). Gbawe Kwatei family Warns Landquards…Gives Police 2 Months Ultimatum to Effect Arrest. An ciro a 2021 daga: https://ghanaiandemocrat.com/gbawe-kwatei-family-warns-landquards-gives-police-2-months-ultimatum-to-effect-arrest/

News Ghana (2015). Head Of Gbawe Kwatei Family Honoured. An ciro a 2021 daga: https://newsghana.com.gh/head-of-gbawe-kwatei-family-honoured/

Tattaunawa da Nii Adam Qwatei Quartey a Gidansa da ke Gbawe Yankin Greater Accra, a ranar 23/8/2021.

Tattaunawa da Sarkin Musulmin dukkan Masarautar Gbawe, Alhaji Sheikh Lamiɗo, Mohammed Jibril Sissy a ranar 23/8/2021


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Sarakuna


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub