Nii Tackie Teko Tsuru II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ga Mantse, Nii Tackie Teko Tsuru IIGa Mantse, Nii Tackie Teko Tsuru II
Hoto:Citi News Room

Gabatarwa

Ga Mance; wanda ake rubuta shi da Ga Mantse a tsarin rubutun ƙabilar Gan ta Ghana, shi ne babban sarkin ƙabilar Ga Mashie. Wannan kujera gadatar ake yi kamar yadda yake a mafiya yawan al’adun gadon sarauta a duniya.

Su kuwa Gan, su ne ƙabilar da suka mamaye Yankin Tsakiyar Ghana; Ghanaian Central Region tare da zamowar Ankara (Accra) babban birnin ƙasar a matsayin helikwatarsu.

Ga Mance, Ni Taki Teko Tsuru na biyu (Ga Mantse, Nii Tackie Teko Tsuru II), shi ne wanda ke zaune daram a kan wannan kujera. Sunan da aka san shi da shi kafi hawa wannan kujera shi ne Dr Kelvin Nii Tackie Abia Tackie.

Karatu

Dakta Taki Teko Tsuru II ya yi karatun digi na farko da na biyu a Jami’ar Kwame Nkrumah (Kwame Nkrumah University of Science and Technology) da ke Ghana. Fagagen da ya samu horo su ne Bachelor of Art da kuma MBA in Strategic Management and Consulting.

Ƙari a kan haka kuma ya yi kwasa-kwasai da dama da suka haɗa da International Business Certificate on Culture daga Jami’ar Kwame Nkrumah da kuma Certificate in Cleaning Science daga Johannesburg, Afirka ta Kudu.

Gogayyar Aiki

  1. Ya kafa kamfanin haƙar ma’adinai mai suna Aenon Artisanal Mining Limited.
  2. Ya zama mataimakin Ɗantakarar Shugaban Ƙasa mai zaman kansa Mr. Jacob Yeboah a kakar zaɓen 2012.
  3. Ya zama mai bayar da shawara a sashen Liberal Studies na Makarantar Fasaha (Kumasi Polytechnic) da ke Kumasi.
  4. Ya karantar da darasin kasuwanci (entrepreneurship) a Makarantar Fasaha ta Kumasi (Kumasi Polytechnic) da kuma Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah (Kwame Nkrumah University of Science and Technology) da ke Kumasi.

Ga Mantse, Nii Tackie Teko Tsuru II
Hoto:Ghana Web

Sarauta

Dakta Kelvin ya zama Ga Mance, Teki Teko Tsuru II a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2015 kamar yadda mujallar Graphic Ghana (2015) ta wallafa a shafinta na Intenet.

Naɗin ya biyo bayan ayyana shi a matsayin sarkin Gan Mashi (Ga Mashie) da ɗaya daga cikin waɗanda alhakin abin yake wuyanta ta yi; Ms Ananaa Annan.

Naɗin da Nii Dr Kwei ya bayyana shi a matsayin cewa abin alfahari ne ga ɗaukacin al’ummar Ga Mashi domin an aje ƙwarya a gurbin da ya dace.

Manazarta:

Ghana Web (2021). Ga Mantse celebrates 50 Birthday with Call for Calm Ahead of Homowo. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.ghanaweb.com/GhanaHomePage/NewsArchive/Ga-Mantse-celebrates-50th-birthday-with-call-for-calm-ahead-of-Homowo-1324153

Grahpic Online (2015). New Ga Mantse Installed. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://www.graphic.com.gh/news/general-news/new-ga-mantse-installed.html


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Sarakuna


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub