Otomfuo Osei Tutu II

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Otomfou Osei Tutu IIAsantehene, Otumfuo Osei Tutu II
Hoto:graphics.com

Gabatarwa

Otumfuo Osei Tutu II, shi ne babban sarkin Asantawa baki ɗaya wanda ake kira Asantehene a Harshen Cui (Twi). Mutum ne shi tsayayye a kan dukkan al’umaran da ya saka a gaba. Yana matuƙar kula da jama’arsa tare kuma da ƙoƙarin kare martabar abin da ya gada. Shi ne sarki na goma sha shida a cikin jerin manyan sarakunan Asantawa. Ya yi karatun zamani kamar yadda ake yi. A wannan rubutu nake fatan baka labarin wannan babban sarki na babbar ƙabilar Ƙasar Ghana.

Haihuwa

An haifi Otumfuo Osei Tutu II a ranar 6 ga watan Mayu na shekarar 1950. Sunansa na yanka shi ne Nana Barimma Kweku Duah. Mahaifinsa shi ne Nana Kwame Boakye-Dankwa mutumin Kantinkyere sannan kuma mai riƙe da muƙamin sarauta mai taken Brehyia Duke kafin rasuwarsa.

Mahaifiyarsa ita ce Nana Afia Kobi Serwaa Ampem II wadda take ita ce Mai Babban Ɗaki wadda a Harshen Asante ake kira Asantehemaa wato Queen Mother a Turance.

Karatu


Asantehene, Otumfuo Osei Tutu II
Hoto:African Research Consult

Ya yi karatu a makaratun da suka haɗa da:

  1. Makarantar Elementary ta Kumasi.
  2. Makarantar Sakandire mai suna Sefwi Wiaso Secondary School.
  3. Makarantar Sakandire mai suna Osei Kyeretwie Secondary School (OKESS).
  4. Babbar makaranta mai suna Erstwhile Institute of Professional Studies wadda yanzu aka cajawa suna zuwa University of Professional Studies da ke Accra.
  5. Makarantar Fasaha mai suna Polytechnic of North London wadda yanzu aka canjawa suna zuwa London Metropolitan University.
  6. Sai kuma Digirin-Digirgir da ya karɓa a matsayin kyautar girmamawa daga Jami’ar London Metropolitan.

Gogayyar Aiki

  • 1981 – 1985: Ya yi aiki a kamfani mai suna Mutual Omaha Insurance Company da ke Toranto a Ƙasar Kanada.
  • 1985 – 1989: Ya yi aiki tare da kamfani mai suna HCPP Stonebridge Bus Garage a London. Daga baya ya kafa nasa kamfanin mai suna Primoda Financial Services Limited da Kilburn High Road, North West London.
  • 1989: Ya sake kafa wani kamfanin mai suna Transpomech Internationa (Ghana) Limited.

Sarauta


Asantehene, Otumfuo Osei Tutu II
Hoto:My News Observer

Otumfou Osei Tutu II ya ɗare karagar babbar sarautar Asantawa a ranar 25 ga watan Afirilun shekarar 1999 biyowa bayan rasuwa kawunsa kamar yadda al’adar Asantawa take cewa ɗan mace (Ƙanwar ko yar sarki) ne ke gadon sarauta.

Manazarta

Amoaka H. K. (2020). Biography of Nana Kweku Duah (Otumfour Osei Tutu II). An ciro a 2021 daga shafin: http://african-research.com/research/biography-of-nana-kweku-duah-otumfour-osei-tutu-ii/

Ankomah B. (2019). Praise Where Praise is Due. An ciro a 2021 daga shafin: https://newafricanmagazine.com/18952/

Ayamaga E. (2021). Otumfuo Osei Tutu II: Kotoko congratulate life patron as he marks 22 years as Asantehene. An ciro a 2021 daga shafin: https://www.pulse.com.gh/sports/football/otumfuo-osei-tutu-ii-kotoko-congratulate-life-patron-as-he-marks-22-years-as/dbclc2z

Wikipedia (2021). Otumfuo Ose Tutu II. AN ciro a 2021 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Otumfuo_Nana_Osei_Tutu_II


Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Sarakuna


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub