Me ka ke nema?


Shafin Farko

Daidaito da ‘Yanci daga Wariya a Ghana


Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sashe na 17: Daidaito da ‘Yanci daga Wariya

Wannan sashe ya zayyano waɗannan tanade-tanade a matsayin kyakkyawan tanadinsa daga cikin Kudin Tsarin Mulkin Ghana a matsayin 'yancin da duk ɗan Ƙasar Ghana yake da shi na Daidaito da ‘Yanci daga Wariya:

 1. Dukkan mutane su zama daidai a gaban doka.
 2. Mutum ba za a mayar da shi saniyar ware ba a bisa dalilin jinsi, ƙabila, launi, asalin ƙabila, addini, mazahaba ko muƙami ko yanayin tattalin arziƙi ba.
 3. Domin buƙatar wannan sashe, “Wareya” na nufin a bayar da kulawa ta daban ga wasu mutane na daban bisa alaƙantawa kawai ko musamman da mabambantan ɓangarori, ko gurin da suka fito, ra’ayin siyasa, launi, jinsi, sana’a, addini ko mazahaba, ta yadda mutanen wani ɓangaren za su fuskanci tawaya ko taƙaitawa wadda mutanen wani ɓangaren basu fuskanta ba ko a basu damammaki ko amfanoni wadda ba a bai wa mutanen wani ɓangaren ba.
 4. Babu wani abu a wannan sashe da zai kare ‘Yan majalisa daga yin dokoki masu ma’ana da suka zama dole a samar:
  1. Saboda aiwatar da ƙudurce-ƙudurce da shirye-shiryen da suke da manufar daidaita walwala, tattalin arziƙi ko ilimi da ke da tawaya a cikin al’ummar Ghana;
  2. Game da al’amuran da ke da dangantaka da riƙo, aure, saki, binne gawa, gado idan aka mutu ko wasu lamura na dokar ɗaiɗaiku;
  3. Domin ɗora taƙaitawa kan mallakar ƙasa ga mutanen da ba ‘yan Ƙasar Ghana ba ko domin aikace-aikacen siyasa da tattalin arziƙin waɗancan mutanen da kuma wasu harkokin da suke da dangantaka da waɗancan mutane; ko
  4. Domin samar da tanadi na daban ga wasu al’ummomi na daban matuƙar an gamsu da yanayinsu na musamman bai zamo tanadi wanda ya yi karo da ruhin wannan kundin tsarin mulkin ba.
 5. Babu abin da za a ɗauka ya yi karo da wannan sashe wanda aka bayar da damar a yi a ƙarƙashin kowanne tanadi na wannan kashi.

Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci
Haƙƙoƙi da ‘Yanci
‘Yancin Rayuwa
'Yancin Walwala
Girmama Ɗan'adam
Kariya Daga Bauta
Yancin Daidaito
Kaɗaikatar Gida
Adalcin Shari’a
Kariya Daga Ƙwace
Muhimman ‘Yanci

Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub