Me ka ke nema?


Shafin Farko

'Yancin Walwala a Ghana


Kundin Tsarin Mulkin Ghana
Hoto: Office Holidays


Gabatarwa

Matashiya:
Dukkan abin da za a karanta daga wannan gaɓa zuwa ƙarshen wannan shafi, fassara ce kai tsaye daga Kundin Tsarin Mulkin Ghana na shekarar 1996 wanda aka ɗauke a shekarar 2021 daga shafin: https://constitutionnet.org

Sashe na 14: Kariyar Walwalar Ɗaiɗaiku

Wannan sashe ya zayyano waɗannan tanade-tanade a matsayin kyakkyawan tanadinsa daga cikin Kudin Tsarin Mulkin Ghana a matsayin 'yancin da duk ɗan Ƙasar Ghana yake da shi na walwala:

 1. Kowane mutum a bashi yancinsa na walwala kuma babu wani mutum da za a tauye wa ‘yancinsa na walwala sai dai a gurare masu zuwa kuma a bisa dacewa da matakan da doka ta bayar da dama:
  1. a yunƙurin aiwatar da hukunci ko umarnin kotu a yanayin babban laifi wanda aka yanke hukunci; ko
  2. a yunƙurin aitawar da umarnin kotu ana ladabtar da shi bisa rashin ladabi ga kotu; ko
  3. bisa dalilin bayyanar da shi a gaban kotu domin aiwatar da umarnin kotu; ko
  4. a yanayin da mutum yake fama da cuta mai yaɗuwa, mutum mai larurar zuciya, mutum mashayin ƙwayoyi ko giya ko kayan maye domin tsaron kansa ko karɓar magani ko domin kare al’umma; ko
  5. bisa dalilin ilimi ko walwalar mutum wanda bai kai shekaru goma sha takwas ba; ko
  6. bisa dalilin kare shigar mutum ta haramtacciyar hanya Ƙasar Ghana, ko aiwatar da kora, ko miƙa wuya ko dukkan wata halastacciyar cire wannan mutum daga Ghana ko bisa dalilin taƙaita wa wannam mutumin bayan halastacciyar shigarsa Ghana a yunƙurin kora ko fitar da shi daga wata ƙasa zuwa wata; ko
  7. da zarar samun wani ƙwaƙƙwaran zargi a kansa cewa ya aikata ko yana yunƙurin aikata babban laifi a ƙarƙashin dokokin Ghana.
 2. Mutumin da aka tsare, ɗaurin-talala, ko aka kulle a sanar da shi nan take, a yaren da zai iya fahimta, dalilan da suka jawo tsarewar, ɗaurin-talalar ko kullewar tasa da kuma ‘yancinsa na ɗaukar lauyan da yake da zaɓi.
 3. Mutumin da aka tsare, ɗaurin-talala ko aka kulle –
  1. bisa dalilin gurfanar da shi a gaban kotu bisa aiwatar da umarnin kotu; ko
  2. da zarar samun wani ƙwaƙƙwaran zargi a kansa cewa ya aikata ko yana yunƙurin aikata babban laifi a ƙarƙashin dokokin Ghana, wanda kuma ba a sake shi ba,
 4. A gurfanar da shi a gaban kotu a cikin awanni arba’in da takwas bayan tsarewar, ɗaurin-talala ko kullewar.
 5. A muhallin da aka tsare, ɗaurin-talala ko kulle mutum a ƙarƙashin ƙanan tanade-tanade (a) ko (b) na babban tanadi na (3) na wannan sashe ba a kuma gurfanar da shi bisa lokacin da ya dace ba, to, ba tare da horo daga kowanne irin hukunci da za a iya kawowa a kansa ba, ya zama an sallame shi ko dai ba bisa sharaɗi ba ko kuma bisa wasu sharruɗa na hankali, waɗanda a keɓe suka haɗa da, sharruɗa na hankali da suka zama dole domin tabbatar da ya bayyana a gaban kotu a wata rana a gaba domin a cigaba da tuhuma ko sauraron ƙara kafin tuhuma.
 6. Mutumin da bisa haramci aka tsare, ɗaurin-talala, ko kulle domin kowane mutum ne ya cancanci biyan diyya daga wancan ɗaya mutumin.
 7. A muhallin da aka yanke tare da zartar masa da hukuncin tsarewa a gidan kaso na wani lokaci bisa wani laifi, dukkan lokacin da ya ɗauka a gurin tsarewa na halas bisa wancan laifi kafin kammala wa’adin hukuncin nasa a ɗauka cewa ana aiwatar da hukuncin tsarewar ne.
 8. A muhallin da mutum ya kamala cikakke ko wani yanki na wa’adinsa ya kuɓuta da ɗaukaka ƙara a kotu, wadda ba kotun ƙoli ba, kotun ta gamsar da kotun ƙoli cewa mutumin da ya kuɓuta an biya shi fansa; kuma kotun ƙolin tana, bayan tantance dukkan hujjoji da takardun shedar kotun da abin ya shafa, bayar da wannan fansa kamar yadda za ta iya tunanin dacewar abin; ko, a muhallin da kuɓutar daga kotun ƙolin ne, tana iya bayar da umarnin a biya fansa ga mutumin da ya kuɓuta.

Shafin Tarihi
Shafin Ghana
Ƙabilun Ghana
Yankuna Ghana

Shugabannin Ƙasa


Tarihin Ghana

Haƙƙoƙin 'Yanƙasa

‘Yanƙasanci

Haƙƙoƙi da ‘Yanci

‘Yancin Rayuwa

'Yancin Walwala


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub