Shafin Farko

Alaƙoƙin Jagoranci


Gabatarwa

Da yawan masu ruwa-da-tsaki a harkar Ilimi basu fahimci ta yadda aka samu dangantaka tsakanin Jagoranci (guidance) da Ilimi (education), saikoloji (psychology), karantarwa (teaching), mahnaja (curriculum), horo (discipline), shugabancin makaranta (school administration), gida (home) da kuma al’umma (community) ba.

Na ɗan yi yunƙurin yin ɗan taƙaitaccen bayani game da wannan dangantaka a wannan rubutu da mai karatu yake karantawa.

Jagoranci da Ilimi

Ilimi abu ne mai matuƙar muhimmanci wajen taimaka wa mutum ya cimma ƙudurorinsa (goals) da burace-buracensa (aspirations) na rayuwa. ‘Yan makaranta kan tafi makaranta don tunaninsu ya zama gaskiya. Iyaye kuma suna kyautata wa makaranta zaton za ta haɓɓaka tunani da hankalin 'ya'yansu. Ilimi shi ke samar da dawamammun ‘yan-ƙasa nagari (wato abin da ake nufi a nan shi ne cewa, ta hanyar ilimi ne kaɗai ake iya samar da ‘yan-ƙasa nagari waɗanda ke amfanar da ƙasa).

Jagoranci (guidance) kuma ta nasa ɓangaren, tallafi ne da wata hanyar taimakon jama’a wacce aka samar da nufin taimakon ɗaiɗaikun mutane su riƙa yanke hukunci cikin fahimta, su kuma yi zaɓi madaidaici wanda ka iya zama mai amfani ga su kansu da kuma jama’arsu (society). Saboda haka ba za a iya raba shirin Jagoranci (guidance programme) da ilimi ba, kuma ana  gudanar da Jagoranci ne a cikin ilimi, saboda haka shi Jagoranci ɗin ya zama wani ɓangare na ilimi. Duka biyun suna da manufa ta taimakon ɗaiɗaikun mutane da kuma al’umma su samu ci gaba. Dukkan biyu suna taimakon ɗaiɗaikun mutane a ciki da wajen makaranta su samu mafita a rayuwa. Kai tsaye muna iya cewa Jagoranci yana taimakon mutum ya haɓɓaka hazaƙarsa a kowanne fannin rayuwa.

Jagoranci da Saikoloji

Saikoloji reshe ne na  kimiyyar walwala (social sciences) wanda ke karantar  ɗan-adam da kuma yadda yake cuɗanya da muhallinsa (environment). Halayen mutum da kuma shi mutum ɗin a kan-kansa, ababe ne masu matuƙar sarƙaƙiya da ba za a iya cin alwashi a kansu ba, haka nan kuma ba za a iya yin bayaninsu a cikin sauƙaƙan kalmomin kimiyyar halittu (biological terms) ba. Suna da manufofi da kuma burace-burace.

Idan har za mu iya fahimtar waɗannan manufofi da burace-burace na mutum, to muna da daɗaɗan kayan marmarin da za mu iya fahimtar halayyar mutum. Fahimtar wannan (halayen mutum), tana da matuƙar muhimmanci ga masu bayar da shawara (counselors) ta yadda za su iya amfani da ita wajen warware matsalolin da masu neman shawara (clients) za su kawo musu.

Babbar dangantakar da ke tsakanin Jagoranci da saikoloji ita ce, taimakawa mutum da cikakkun abubuwa (resources) da hanoyin (procedures) da zai yi amfani da su a kowanne fanni na ilimi. ‘child psychology’, ‘industrial psychology’, da gwaje-gwajen saikoloji (psychological test), dukkansu basu yiwuwa sai da jagoranci. Saboda haka jagoranci yana buƙatar mai bayar da shawara ya samu ilimin saikoloji. Saboda haka ana iya ɗaukar jagoranci a matsayin saikoloji a aikace. Jagoranci zai taimaki mai bayar da shawara (counselor) ya aiwatar (implement) da matakan koyo (learning process) waɗanda ke da ƙudurori na taimakon mutum ya gina kansa, ya fahimci kansa, ya kuma samu kyakkyawar cuɗanya da sauran jama’a. Ilimin da ɗalibai suka samu a aji na matakan ci gaba (developmental stages), da kuma siffofi ko ɗabi’un (characteristics) kowane mataki (stage), suna taimaka wa aikin mai bayar da shawara ya kai ga nasara.

Babbar gudunmawar masana saikoloji da fishiyatirist (psychiatrist) ga jagoranci, ita ce nazariyoyin koyo (learning theories) da suke da su. Kamar yadda masana saikoloji ke siffanta koyo a wasu keɓantattun kalmomi, mai bayar da shawara (counselor) yana iya fahimtar cewa mutum ya koya ko bai koya ba. Saikolojin ilimi (educational psychology) yana da masaniya game da hanyoyin aiwatar da dabarun kimiyya (scientific methods) wajen nazartar halayen mutane a muhallin koyo da koyarwa (instructional settings). Shi kuma mai bayar da shawara (counselor), yana amfani da wannan ilimi a aikace wajen bayar da shawarar da ta shafi harkar ilimi ga malamai da ɗalibai.

Jagoranci da Karikulum

Ana iya fassara karikulum da nagartaccen tsarin darasi wanda aka shirya shi dan faɗaɗa ilimi (knowledge) da gogayyar (experience) ɗalibi. Kowa ya yarda cewa karikulum shi ne muhimmin abin da ke taimakawa makaratu su cimma manufofinsu.

Akwai dangantaka ta ƙut-da-ƙut tsakanin jagoranci da ayyukan karikulum (curriculum activities), saboda sun yi tarayya a manufarsu ta taimakon mutane su kai ƙololi wajen amfani da kuma fahimtar kansu. Dukkansu suna da damuwa ta ganin mutane da kuma al’ummu sun cimma manufofinsu. Jagoranci da karikulum dukkansu muhimman ɓangarori ne masu dangata da juna a cikin harkar ilimi. Ana buƙatar dukkansu wajen samar da darrusa da kuma gogayyar da suka dace da haƙanin buƙatun mutane da kuma al’umma waɗanda ke caccanjawa da canjin zamani.

Jagoranci yana bayar da gudunmawa wajen samar da karikulum (curriculum development), saboda buƙatun ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙungiyoyi na faɗaɗa karikulum (curriculum extension) da ayyukansa, ana iya ganinsu a bayyane ta hanyar bayar da shawara (counselling), gwaji (testing), tsari (planning), bibiya (follow-up), da sauran ayyukan jagoranci. Mai bayar da shawara (counselor) zai iya zama kafar da ƙwararru a fannin karikulum (curriculum specialist) za su samu gamsassun bayanai waɗanda ke cike da ƙwazon ɗaiɗaikun ɗalibai, nasarorinsu, nagartarsu, gajiyawarsu, burace-buracensu, tarihin iyali, ƙarfin tattalin arziƙin iyayensu, da sauran abubuwan kulawa wajen shirya karikulum.

Masu bayar da shawara suna taimakawa ɗalibai su zaɓi tsarin karikulum ɗin da zai dace da su ya kuma taimaka musu wajen haɓɓaka cuɗanyarsu da kuma yin kyakkyawan zaɓin sana’a wanda suke buƙata su rayu cikin al’umma mai sarƙaƙiya.

Jagoranci shi ya fi taimakawa ɗalibai wajen tsara manufofinsu na ilimi da sana’a fiye da dukkan wani shiri da ke da wannan manufar. Saboda haka, abu ne mai matuƙar muhimmanci a riƙa saka masu gudanar da shirin jagoranci a makarantu cikin harkokin samar da karikulum.

Jagoranci da Horo

Horo na iya zama hanya da malamai ke amfani da ita a aji, tana iya zama wani horo (training) da ake yiwa mutane dan su bi doka-da-oda, kuma wasu matakai da hukuma ta samar sannan kuma tana iya zama ladabtarwa (punishment), Okon (1984). Ana kuma iya kallon horo a matsayin yunƙurin sake gina halayyar masu gurɓatacciyar halayya wacce damuwa ta haifar (misali, sake dawo da yaran da damuwa ta saka su aikata halayar shaye-shaye zuwa daina aikata halayyar). Haka nan ana iya kallon horo a matsayin rigakafin da ke samar da ingantaccen ci gaban jama’a ta hanyar samar da yanayi mai kyau wanda ke ƙarfafa guiwa, taimako, da halasta kyawawan halaye masu cike da lafiya da jin daɗi, wannan ya fi mayar da hankali wajen gina ɗaiɗaikun mutane (self-development of individuals).

Ta ɓarayin jagoranci, ana kallon horo a matsayin hanyar gyara kura-kuren jama’a, maimakon hanyar toshe gurɓatacciyar cuɗanya. Horo a matsayin ladabtarwa kawai, ya kamata ya zama hanya ce ta gyara ko hanyar samar da ci gaba. Ya kamata a samu nagartattun hanyoyin canza gurɓatattun halaye zuwa halayen fahimtar kai da ciyar da kai gaba.

Cuɗanya kalmomin jagoranci (guidance) da kuma horo (discipline) a guri guda, sun yi yunƙuri haifar da ruɗani. Misali, ya kamata masu bayar da shawara su samu kansu a cikin kwamatin aiwatar da horo? Ya kamata su riƙe muƙamin yanke hukunci game da halayen ɗalibai? Waɗannan da ma wasu tambayoyi da suka yi kama da su, an daɗe ana cece-ku-ce a kansau. Ga hujjojin wasu masana masu ra’ayin cewa bai kamata masu bayar da shawara su saka hannunsu cikin harkokin horo ba, da kuma hujjojin masu ra’ayin cewa ya kamata masu bayar da shawara su saka hannunsu cikin harkokin horo:

Ya kamata mai bayar da shawara ya saka hannunsa cikin horo

 • Waɗanda ke aikata ba-dai-dai ba suna da buƙatar shawarwarin da za su ɗora su a kan turbar da za ta daidaita musu tunaninsu da kuma ayyukansu.
 • Matuƙar ba a shigar da masu bayar da shawara cikin harkokin horo ba, to amfanin jagoranci ya ragu, saboda manufarsa ita ce inganta tarbiyyar ɗalibai.
 • Akwai buƙatar masu bayar da shawara su gano dalilai masu gyaruwa waɗanda ke haifar da aikata laifuka (wato dalilan da ke jawowa a aikata laifuka kuma ya zama waɗannan dalilan za a iya gayarasu).
 • Mafi kyawun aikin horo shi ne kariya (wato ya kare mutum daga aikata laifi), haka nan kuma dukkan ƙwarewar mai bayar da shawara da dabarunsa sun ƙare a kan aikin bada kariya (daga aikata laifi).
 • Burin jagoranci shi ne ladabtar da kai (yi wa kai tarbiyya; ya zamo mutum a kan-kansa zai iya hana kansa aikata abin da ya ke ganin bai dace ya aikata shi ba, duk yadda abin ya kai da kyau ko daɗi), sanin kai (mutum ya san matsayinsa ta kowace fuska kamawa daga ƙarfin jiki, lafiyar jiki, ƙarfin tattalin arziƙi, kaifin ƙwaƙwalwa, basira, hazaƙa, zalaƙa da sauransu), ciyar da kai gaba, da kuma haɓɓakar mutum.
 • Gyaran tarbiyya (wannan na nufin gyara tarbiyyar yaron da tarbiyyarsa ta gurɓace) yana buƙatar ƙa’idojin jagoranci, dabarun saikoliji na gano matsala, da kuma ƙwarewa ta hanyar karatu wanda a makaranta kawai mai bayar da shawara yake iya samu.

Bai dace mai bayar da shawara ya saka hannunsa cikin harkar horo ba

 • Bibiya da kuma aiwatar da dokoki dan kyautatuwar abubuwa (tarbiyya) aikin shugabanni ne.
 • Shigar mai bayar da shawara cikin harkokin horo, zai sa a kalle shi da siffar hukuma wanda hakan kuma zai iya zama barazana ga karɓuwarsa wajen mutane, da kuma gudunmawarsa ta bayar da shawara.
 • Dukkan matsalolin horo suna da buƙatar zuzzurfan bincike wanda hakan kuma ka iya ragewa masu bayar da shawara lokacinsu na bayar da shawara.
 • Bayar da shawara na buƙatar ‘yantacciyar dangantaka maimakon tursasawa wacce take siffa ce ta bayar da horo; abin da ake nufi a nan shi ne cewa akwai buƙatar ya zama dangantakar da ke tsakanin mai bayar da shawara da ɗalibai dangantaka ce mai ‘yanci ba ta tursasawa ba, saɓanin mai bayar da horo wanda shi ana binsa ne saboda tsoron hukunci.
 • Horon da ke tursasa tarbiyyar bai-ɗaya (kyakkyawan aikin da ya zama dole kowane ɗanmakaranta ya yi) abu ne na jama’a. Amma jagoranci abu ne na ɗaiɗaikun mutane kuma a sirrance.
 • Horo abu ne na gama-gari (abin da ya shafi kowa), ko dai a makaranta ko a cikin al’umma, amma shi kuwa jagoranci ya fi karkata ga ɗaiɗaikun mutane.
 • Ana siffanta horo da kalmomin ƙayyade dokoki, tursasawa, bin doka da oda, danƙarawa, biyayyar dole da sauransu. Ita kuwa bayar da shawara ana siffanta ta da samar da ci gaba, ƙarfafar sanin kai, gina kai, yarda da kai, da sauransu.

Gudunmawar mai bayar da shawara a harkokin horo

Babu kokwanto game da saka hannun mai bayar da shawara cikin harkokin horo a makaranta. Haƙiƙa yana da muhimmiyar rawar da zai taka a cikin harkokin horo. Amma shigar tasa ta musamman ce, saboda zai taimakawa ɗalibai su bankaɗo, su tantance, su fahimta, sannan kuma su gyara laifuffukansu. Haƙiƙanin aiwatar da horon kuma aikin shugabanni ne.

Bisa la’akari da wannan ra’ayin na buƙatar saka hannun mai bayar da shawara cikin harkokin horo, malamai za su riƙa tura ɗalibai zuwa karɓar shawarwari tun kafin lamari ya lalace har ya kai ga ladabtarwa. Wannan kuma na buƙatar lura da kuma gogewa, idan kuma ba haka ba to zai zama ana tursasawa ɗalibai zuwa karɓar shawara. A bisa wannan ra’ayin, bayar da shawara zai karkata ne zuwa aikin bayar da kariya ta hanyar taimakon mutane su:

 • Fahimci halayensu.
 • Su koyi ladabtar da kansu (self-control) tun kafin faruwar manyan matsaloli. A nan ana nufin mutum ya zama zai iya hana kansa aikata duk abin da bai dace ba. Misali, mutum ya kafawa kansa ƙa’idar zuwa aji a kan lokaci, wannan zai hana shi yin latti. Bibiyar laifuffukan mutane ko kuma tsunduma cikin dabarbarun haifar da ruɗanin rayuwa duka ba aikin mai bayar da shawara a ciki. Aikinsa shi ne ya bijiro da wannan halayyar (wacce ba a so) ta wasu fuskoki ga mai karɓar shawara, sannan kuma ya samar masa da kyakkyawar mahanga mai amfani ga wannan halayyar da kuma shi kansa. Ya taimaka masa ya fito da wata halayya mai ingantaccen daidaito tsakanin daidai da rashin daidai. Shi bai zamo wanda aka zalunta ba kuma bai zama mai zalunci ba, sai dai, halayya wacce zai ce “Na aikata, kuma na san laifina ne”.
 • Masu bayar da shawara za su iya biyan buƙatun ɗalibai sosai idan ba su zamo masu aiwatar da hukuncin horo game da halayen ɗalibai na bijirewa dokokin makaranta ba. A riƙa ƙarfafa cewa wannan ba yana nufin masu bayar da shawara su riƙa bibiyar laifuffukan ɗalibai ba ko kuma su riƙa nisantar tattauna waɗannan matsalolin a wajen ganawar bayar da shawara (counseling interview). Alaƙar bayar da shawara tana buƙatar ɗalibi ya riƙa bayyana damuwarsa kai tsaye ba tare da jin tsoron za a ladabtar da shi ko kuma tona masa asiri ba. Koda kuwa matsalar ta iya kasancewa ta haɗa da malamai. A irin wannan yanayin mai bayar da shawara baya fitowa a matsayin mai horo, sai dai kawai suna da hannu a cikin kyakkyawan tsarin ladabtarwa a makaranta.

Jagoranci da Shugabancin Ilimi (Guidance and Educational Administration)

Shugabanci na wanzuwa ne dan ya taimakawa makaranta ta cimma manufofinta (goals). Mahangarsa baki ɗaya makaranta ce, kuma ya samu ne dan ya tallafi makarantar baki ɗayanta.

Babbar damuwar shugabannin makaranta ita ce ingancin tsarin makaranta. Suna ƙoƙari wajen ganin an samu wadatattun ma’aikata a makaranta dan su aiwatar da aikin da ya dace. Suna tabbatar da cewa an samu wadatattun gine-gine kuma an kula da su dan ɗalibai su samu wajen rayuwa. Suna tabbatar da cewa an ciyar da ɗalibai, an inganta yanayinsu, ana kuma sufurinsu zuwa makaranta da komawa. Suna mayar da hankali wajen ganin cewa abin da za a girba bayan hidindimun shekaru goma sha biyu ya gamsar da al’umma.

Jagoranci a ta ɗaya ɓangaren kuma yana da alhakin kariya da kuma adana manufofin ɗaiɗaikun jama’a. An tsara shi ya taimaka wa ɗaiɗaikun jama’a su cimma manufofinsu. Da yawan jama’a suna yiwa jagoranci kallon abu ne na ɗaiɗaikun mutane (wato ya fi karkata ga buƙatun mutane a ɗaiɗaiku) saɓanin shugabanci wanda shi ya karkata ga makarantar kacokaf.

Duk da cewa, buƙatun ɗaiɗaikun jama’a da kuma na makarantar a sarƙaƙe suke ba za su rabu ba. Jama’a su ke cika makarantu (wato ɗaiɗaikun jama’a suke samar da makaranta) haka nan kuma ɗaiɗaikun jama’a na samun biyan buƙata ta hanyar tallafin wasu. Amma a nan jagoranci (guidance) bai zamo shugabanci (administration) ba, kuma kar a fassara shi haka nan. Shugabanci yana aiki ne dan ya samar da kayan aiki da kuma makoma ga ma’aikata (organization) dan ya zama ta cimma manufofinta yadda ya dace.

Shugabanci shi ke samar da yanayi mai inganci ga karatu wanda ya haɗa da mutum ya san kansa da kuma duniyar da yake ciki. A nazarce, dukkan biyun suna samar da ‘yancin tambaya, bincike da kuma aiwatarwa, tare kuma da kulawa da buƙatun ɗaiɗaiku. A zahirance makarantu da kuma al’umma suna ƙarfafar ‘yanci da kuma nagartattun ayyuka. Saboda haka jagoranci da kuma shugabanci suna ƙoƙarin samawa ɗaiɗaikun ɗalibai tunane-tunanen ayyukan ɗaiɗaikun jama’a a cikin al’umma.

Zaton Masu Bayar da Shawara ga Shugabancin Makaranta

Ana saka tsammanin, masu bayar da shawara suna tsammanin cewa bayan ɗawainiyoyin shugabanci wajen shugabantar shirin bayar da shawara, za kuma su samar da kayayyakin aiki, samar da isassun kuɗaɗe da kuma ƙwararrun mutane, da kuma sanar da jama’a game da shirin. Saboda haka suna tsammanin cewa:
 1.  Shugabannin makaranta za su samar da ƙalu-bale cikin shugabancinsu.
 2.  Shugabannin makaranta za su tsayu a kan shirye-shiryen jagoranci waɗanda suka yi tarayya a ciki wajen manufa da kuma alaƙa. Saboda kasantuwar ayyukan da basu da dangataka da juna ba za su taɓa samar da shiri ba.
 3.  Shugabannin makaranta za su yi amfani da su a matsayin jama’a (group) masu kawo haɓɓakar shirin jagoranci a nan gaba.
 4.  Shugabanni su samu dawamammiyar halayyar tantancewa game da shirin.
 5.  Shugabannin makaranta su matsa/dage game da wanzuwar shirin, kamalarsa da kuma daidaito.
 6.  Shugabanni su rage wahalhalun da ke tattare da aikin shugabanci, sannan kuma su sauke musu nauyin samar da ɗawainiyoyin ƙwararru.

Zaton Sugabannin Makaranta ga Masu Bayar da Shawara

Da farkon farawa, shugabannin makaranta suna tsammanin masu bayar da shawara su gogar da jama’a sannan kuma su kula da ɗalibai. Haka nan kuma suna tsammanin masu bayar da shawara su samar da hanyoyin da ɗalibai za su samu taimako wajen fahimtar kansu da kuma sauran jama’a, ta ɓarayin gwada fahimtarsu ta samun abubuwa daga wajen makaranta, da kuma zaƙulo ra’ayuyyukansu da kuma abubuwan da za su iya yi. Ta yin haka nan, za a gamsu cewa masu bayar da shawara suna bada gudunmawa wajen cimma manufofin makaranta.

Haka nan dai shugabannin makaranta suna tsammanin masu bayar da shawara za su wadatar da su da ƙwararran hujjoji game da ƙwazon ɗalibai, burace-buracensu da kuma ci gabansu a makaranta da kuma ayyukansu na bayan gama makaranta. Haƙiƙa wannan zai taimaka wa shugabanni su nazarci hanyoyin da malaman makaranta za su ga matsaloli da kuma buƙatun ɗalibai sannan kuma su agaza musu wajen samar da buƙatun ɗalibai a mabanbantan matakan ci gaba.

Shugabanni suna tsammanin masu bayar da shawara su riƙa yin aikin ƙwararru masu hankali. Suna tsammanin masu bayar da shawara su haɓɓaka matsayinsu, sannan su riƙa bibiyar ayyukansu a-kai-a-kai dangane da abubuwan da suka yi daidai, da kuma waɗanda suke buƙatar a inganta su. Suna tsammaninsu su riƙa karanta rubututtukan ƙwararru da kuma halartar ayyukan gamayya na ƙwararru da kuma ƙungiyoyi.

Babbar manufar shugabanci ita ce yunƙurin sadar da tsakanin (coordination effort) jama’a su cimma manufofin ma’aikata. Wannan na nufin ayyukan shugabanni ya karkata wajen tallafawa koyarwa da koyo a makaranta, sannan kuma ya damu da yadda baki ɗayan ayyuka ke gudana da ma yadda ake aiwatar da su ciki kuma har da aikace-aikacen jagoranci (guidance services). Kai tsaye, shugabanci yana wanzuwa ne dan ya tunkuɗa makaranta ta cimma manufofi da kuma ƙudurorinta wanda shi kuma jagoranci a wuyansa nauyin kariya da kuma killace ra’ayin ɗaiɗaikun wajen cimma burinsu ya ke. Saboda haka, dukkan biyun suna da manufa ta ƙarfafar ‘yancin tambaya, zaƙulowa tare kuma da aiki. Dangantakar ta karkata ga tsaurarawarsu da kuma kulawarsu ga ɗaiɗaikun jama’a.

Dangantakar Jagoranci da Gida/Al’umma (Guidance, the Home and the Community)

Makaranta da gida, abubuwa ne masu matuƙar tasiri ga rayuwar yara. Tasirin nasu kuma zai yi matuƙar ƙaruwa idan suka yi aiki tare ko kuma suka sarƙafe da junansu wajen ganin sun kawar ko kuma sun rage dalilan da ke kawo cikas ga karatun yara, sannan kuma su daidaita yaran da tuni suka fara bayyanar da halayen ƙi.

Makaranta tana da matsayi mai girma wajen baiwa matasa shawara. Suna da dangantaka ta ƙut-da-ƙut kuma mai ɗorewa tsakaninsu da yara kuma cikin lokaci mai tsawo. Makaranta ta na karɓar yara tun suna da ƙananan shekaru, kuma ta na da kyakkyawar manufar taimakawa yaran su zama ‘yan’ƙasa nagari masu amfani a cikin al’umma. Saboda ita makaranta kusan tana sarrafa kowane yaro, saboda haka masu bayar da shawara an yi musu horo akan cuɗanya da matasa sannan kuma da warware matsalolin matasa, su na da kyakkyawar damar da babu wata hukumar da ke da ruwa-da-tsaki wajen jagorancin matasa da cigabansu take da shi. Makaranta ita ce kaɗai cikin irin hukumomin da ke hulɗa da yara masu tasowa.

Kasancewar damuwar iyaye da makaranta ita ce jagoranci (guidance), to, ba abu ne mai yiwuwa ba wani daga cikinsu ya samar da nagartaccen tsarin jagoranci shi kaɗai. Nagartaccen tsarin shirin jagoranci zai samu ne kawai idan makaranta da gida suka haɗa hannu wajen tsara ayyuka da kuma cin/shan alwashin aiwatar da waɗannan ayyukan tare. Shirin jagoranci zai samar da bayanan sana’a ga iyaye wanda zai taimaka musu wajen yiwa ‘ya’yansu kyakkyawan tsari cikin sani.

Jagoranci zai kuma taimaka wa iyaye su fahimci shekarun ƙiriniya (adolescents) sosai, sannan kuma ya basu cikakkiyar masaniya game da tunanin matasa a kan abin da ya shafi walwala/cuɗanya (social) da kuma sana’a. Masu bayar da shawara za su iya taimakawa iyaye su nemi taimako daga hukumomi masu zaman kansu ko na gwamnati waɗanda ke da ruwa-da-tsaki wajen warware matsalolin yara da suka shafi tawaya ta zahiri (naƙasa) ko ta tunani (kamar shaye-shaye, dolanci, da sauransu). Ta hanyar tuntuɓar iyaye, mai bayar da shawara zai iya taimaka musu su samu kyakkyawar fahimtar dangantakar iyaye (parental relationship) da kuma kintsa mata, da tasirinta a akan ‘ya’ya. Masu bayar da shawara za su iya zama kafar sada tsakanin iyaye da malaman makaranta.

A wani cigaban kuma, za a iya kallon dangantakar jagroanci da gida/al’umma ta waɗannan fuskokin:

 1. Alhakin tattalawa, ciyarwa, tufatarwa, da kuma samar da muhalli. A wannan matakin, jagoranci (guidance) da kuma gida suna bayar da gudunmawa wajen ci gaban yara a matsayinsu na mutane ta hanyar wadata yaro da abubuwan buƙata na yau-da-kullum, saboda haka suka zama abubuwan da basa rabuwa, tun da shi jagoranci abu ne da ake yinsa a gida da kuma makaranta.
 2. Iyaye da ‘ya’ya kullum a cakuɗe suke, saboda haka kenan ana aiwatar da jagoranci. Masu iya magana sun ce, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.
 3. Jagoranci (guidance) yana zaƙulo buƙatun yara sannan ya sanar da iyaye a lokutan taron iyaye da malamai (PTA meetings), ko kuma a ranakun bayar da kyaututtuka. Saboda haka jagoranci ya zama kafar sadarwa tsakanin makaranta da gida.
 4. Masu bayar da shawara suna taimaka wa iyaye wajen ƙulla dangatakar cuɗanya a cikin al’umma, misali tura mutum zuwa ga wata hukuma a cikin al’umma da kuma tura ɗalibai zuwa ga wani ƙwararre da ke wajen makaranta.
 5. Mai bayar da shawara yana zama na dogon lokaci tare da yaro, misali yaro mai naƙasa wanda ya ke buƙatar kulawa, ƙauna da ja-a-jika.
 6. Ya kamata al’umma ta bayar da gudunmawa wajen ƙarfafar shirin jagoranci ta hanyar bayar da tallafin kuɗi da kuma kayan aiki, misali samar da kayayyakin motsa jiki, guraren shan-magani, haka nan su kuma masu bayar da shawara su kusanta kansu da iyaye.

A taƙaice, ƙarfafa dangantakar iyaye, makaranta, da kum al’umma abu ne mai tarin fa’ida ga shirin jagoranci. Nagartar haɗin kansu ta dogara da fayyacacciyar sadarwa da kuma yadda za su samar da kayayyaki tare dan inganta shirin jagoranci. Ba sai an ce ya zama dole a samu kyakkyawar fahimtar juna tsakanin makaranta, iyaye, da kuma al’umma dan tallafawa juna ba.

Wannan rubutu, fassara ce ta littafin karantarwa na Adamu Bagudu, Ph,d., Kaduna Polytechnic.