Hajiya Hadiza Bala Usman

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hadiza Bala UsmanHajiya Hadiza Bala Usman
Hoto: Jaridar Today


Gabatarwa

Kyan gida da Magaji! Hajiya Hadiza Bala Usman ta gaji mahaifinta zamowarta ‘yar siyasa kuma ‘yar fafutikar ƙwatar ‘yancin bil’adam “Na tashi na ji mahaifina yana ƙalu-balantar gwamnati tare da abubuwan da ke gudana” a-ta-bakin Hajiya Hadiza Bala Usman da ta ke zantawa da mujallar Metropole a shekarar 2016.

A yanzu haka (2020), ita ce ke riƙe da muqamin babbar jami'ar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya.

Mahaifinta Dr. Yusuf Bala Usman, gogaggen malamin jami’a ne, fitaccen ɗan siyasa sannan kuma sananne a harkar fafutikar ganin adalci ya tabbata a Najeriya.

Hajiya Hadiza Bala Usman na ɗaya daga cikin matan duniya guda ɗari da suke da tasiri a wannan zamanin. Ita ce ta ƙirƙiri ƙungiyar nan mai rajin ganin an dawo da ‘yan’matan Chibok da aka sace.

Haihuwa

An hafi Hadiza Bala Usman a Unguwar Hanwa da ke Zariya a Jahar Kaduna ta Najeriya, a cikin shekarar 1976. ‘Ya ce ga shahararren malamin jami’ar nan kuma fitaccen ɗan fafutikar ‘yancin bil’adam sannan kuma tsohon sakataren gwamnatin jahar Kaduna a zamanin mulkin gwamna Abdulƙadir Balarabe Musa a jamhuriyar siyasar Najeriya ta biyu, a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PRP wato marigayi Dr. Yusuf Bala Usman.

Karatu

Hadija Bala Usman ta yi karatun firamare a ‘ABU Staff School’. Bayan gama firamare kuma ta shiga sikandiren ‘ABU Demonstration Secondary School’. Sannan kuma ta shiga Jami’ar Ahmadu Bello inda ta samu digirin farko a fannin gudanarwar kasuwanci (Business Administration) a shekarar 2000,  duk a garin Zariya.  

Daga baya ta samu zuwa ƙasar Ingila, inda ta yi karatun digiri na biyu  a fannin ‘Development Studies’ a jami’ar Leeds (University of Leeds) da ke United Kingdom, a shekarar 2009.


Hajiya Hadiza Bala Usman
Hoto: The Whistler NG

Gogayyar Aiki

Tun bayan gama karatun digirin farko, Hajiya Hadiza ta fara aiki da ƙungiya mai zaman kanta ta ‘Centre for Democratic Development and Research Training (CEDDERT)’ da ke Zariya a shekarar 1999 a matsayin jami’a mai taimako a fannin nazari (Research assistant). Ta kuma yi aiki da ofishin ‘Bureau Of Public Enterprises (BPE)’ daga shekarar 2000 zuwa 2004.

Ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa-da-ƙasa mai suna UNDP ta ɗauki Hajiya Hadiza aiki tun daga watan Oktoba na shekarar 2004 har zuwa watan Janairu na shekarar 2008, inda ta yi aiki a matsayin mai taimakon musamman ga ministan babban birnin tarayya (Special Assistant to the FCT Minister on Project Implementation) a fannin aiwatar da ayyuka, ƙarƙashin Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (Federal Capital Territory Administration [FCTA]).

Sannan kuma tun daga shekarar 2011, ita ce daraktar tsare-tsare ta ƙungiyar nan mai rajin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci (Director of Strategy for the Good Governance Group (3G)).

Ta riƙe muƙamin shugabar ma’aikatan jahar Kaduna tun daga shekarar 2015 har zuwa 2016, naɗin da ya saka ta ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami tun da aka ƙirƙiri ofishin a shekarar 1999. Mai girma gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i shi ya yi mata wannan muƙamin.

A ranar Litinin 11 ga watan Juli (July) na shekarar 2016, shugaba Muhammadu Buhari ya yi mata muƙamin babbar jami’ar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa (Director Nigerian Port Authority (NPA)), muƙamin ta ke riƙe da shi daram har zuwa yau ɗin nan (2020).


Hajiya Hadiza Bala Usman
Hoto: Naira Land

Gudunmawa

Hajiya Hadiza Bala Usman ta daɗe tana bayar da gudunmawa a fannonin rayuwa daban-daban, musamman fafutikar ganin an yi adalci a ƙasa, da kuma ƙwatowa marasa gata haƙƙinsu. Ita ce ta kafa ƙungiyar nan mai rajin ganin an dawo da ‘yan’matan Chibok mai suna ‘Bring Back Our Girls’ a shekarar 2014 bayan da aka sace sama 300 a garin Chibok da ke cikin Jahar Borno a Najeriya. “Ba zan iya zama a gida ina mai jin cewa wannan abin bai shafe ni ba”, a ta bakin Hajiya Hadiza.

Kyaututtukan Girmamawa

Hajiya Hadiza Bala Usman ta samu lambobin yabo da kyaututtukan girmamawa daga gida da kuma ƙasashen waje. Daga cikin irin waɗannan kyaututtuka akwai:

  1. Zamowarta ɗaya daga cikin mata ɗari mafiya tarisi a duniya a shekarar 2014 (Most influential women of 2014). Jaridar Financial Times.
  2. Mata masu zaburantarwa a 2014 (Inspiring Woman of 2014). CNN.
  3. Zamowarta ɗaya daga cikin mata ɗari baƙar fata masu tasiri a duniya 2014 (The 100 most influential black women in the world in 2014). Ebony Magazine.

Manazarta:


Adi F. (2015). El-Rufai names Hadiza Bala Usman, first female chief of staff. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://thenewsnigeria.com.ng/2015/06/el-rufai-names-hadiza-bala-usman-first-female-chief-of-staff/

Metropole Magazaine (2016).Hadiza Bala Usman: Her Father’s Daughter. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://metropole.ng/index.php/promo/item/1923-hadiza-bala-usman-her-father-s-daughter

Wallis W. (2014). Women of 2014: Hadiza Bala Usman. An ciro a shekarar 2016, dagashafin: https://neɗt.ft.com/content/08738682-7fa7-11e4-adff-00144feabdc0

Wikipedia (2016). Hadiza Bala Usman. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Hadiza_Bala_Usman

Wikipedia (2020). Hadiza Bala Usman. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Hadiza_Bala_Usman

Shafin Tarihi


Mashahuran MutaneTura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub