Rumbun Ilimi - Alamomin Rubutu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alamomin Rubutu


Gabatarwa

  1. Aya, tana da nau’uka uku:
    • Babbar aya (.): Alama ce ta cikar Jimla da kuma bayar da damar tsayawa cik, ko kuma ƙarewar zance. Dokar rubutun Hausa a kanta ita ce, cewa, dukkan harafin da zai biyo bayanta dole ya zama babban baƙi. Misali:
    • Isa ya ci tuwo.
    • Ɗanbarno ya zo da safe. Shi ya bar wannan hular  a nan.
    • Ayar tambaya (?): Alama ce da ke nuna cewa, dukkan jimlar da ta ƙare da wannan alama to tambaya ce. Misali:
    • Mene ne a ciki?
    • Ka shiga Rumbun Ilimi kuwa a yau?
  2. Ayar motsin rai (!): Ana saka ta a bayan kalmar da ke nuna sosuwar rai, wacce ka iya zama ta farin ciki, baƙin ciki, razani, da sauransu. Misali:
    • Ahayye! Allah ya kawo mu.
    • Hahaha! Allah sarkin daɗi.
    • Wayyo! Ku kawo mani agaji.
  3. Tagwan Ayoyi (:): Tana da hukunce-hukunce kamar haka:
    • Cikakkiyar dakatawa.
    • Kawo maganar wani. Misali, Musa ya ce: “Ku sayo min gyaɗa idan za ku dawo”.
    • Jero sunayen abubuwa. Misali, Ado yana sayar da kayayyaki irinsu: Littafi, alƙalami, jaka da sauransu.
  4. Waƙafi (,): Alama ce ta dakatawa ta ɗan ƙaramin lokacin da bai wuce mai karatu ya shaƙi nunfashi ba. Ana ɗiga waƙafi a gurare kamar haka:
    • Gaɓar magana.
    • Gaɓar jimla.
    • Guraren da ake rarraba sunaye a cikin jere. Kamar ka ce Ado, Idi, Musa da Binta ɗalibai ne masu hankali. Idan aka lura a nan, waƙafi ne ya bambanta mana sunan Ado da na Idi. Dokar rubutu ta ce dukkan harafin da zai biyo bayan waƙafi dole ya zama ƙaramin baƙi.
  5. Waƙafi mai ruwa (;): Alama ce ta gajeruwar dakatawa. Ana ɗiga ta a tsakanin jimloli biyu masu kama da juna waɗanda kuma kalma ta biyun ke zama cikwaton ta ɗaya. Misali: Babu wanda zai yi wannan aikin sai yara; domin su ne basu da hankali. Sannan kuma ƙaramin baƙi ne yake biyo bayanta.
  6. Zarce (…): Ayoyi ne guda uku. Alama ce da ke nuna rashin ƙarewar zance. Suna iya zuwa a farko, tsakiya ko ƙarshen rubutu. Sannan kuma babu wata dokar rubutu da ta ce ga matsayin harafin da zai biyo bayanta. Kenan babba ko ƙaramin baƙi kowane na iya biyo bayanta. Ta zama abin da ake cewa, cinsa banza, barinsa banza kenan. Idan har mutum baya shiga shafin Rumbun Ilimi akai-akai, lallai…
  7. Baka biyu (): Alama ce da ake amfani da ita a gurare kamar haka”
    • Ƙunshe ƙarin bayani game da rubutun da ya gabace ta a ciki. Misali, Rumbun Ilimi (softuwayar kwamfuta cikin Harshen Hausa zalla), yana ɗauke da darrusa masu muhimmanci.
    • Haka nan kuma ana amfani da baka biyu wajen rubuta haƙiƙanin lambobin da aka rubuta adadinsu a cikin zance. Misali, jiya sun samu kuɗi har Naira dubu shida (N6000).
    • Wajen kafa hujjar wanda ya faɗi magana a cikin zance. Misali, Hausa tana da kalmomi masu gaɓa ɗaiɗai da yawan gaske (Yahaya, Zariya da ‘Yar’aduwa 2007).
  8. Alamar zancen wani (“”): Alama ce da ake ƙunshe gundarin maganar da aka hakaito daga wani mutum a cikin zance. Misali, shi fa dama sai da ya ce: “Kowane ɗalibi ya kawo min nasa aikin da kansa”. Dokar rubutun Hausa ta wajabta fara rubuta harafin farko na abin da aka ƙunshe a ciki ya zamo babban baƙi.
  9. Karan ƙori (-): Alama ce da ke ƙulle tsakanin kalmomi biyu su yi aikin kalma ɗaya. Ana ɗiga wannan alama a gurare kamar haka:
    • Gauraya ko haɗe kalmomi mabambanta. Misali: Bigi-bagiro, gam-da-katar da sauransu.
    • Ana amfani da ita wajen maimaita kalmomi iri ɗaya. Misali: daban-daban, akai-akai da sauransu.
  10. Kara jirge (/): Alama ce da ake amfani da ta wajen bayar da zaɓin abu guda daga cikin jeri. Tana aiki ne a matsayin ko. Misali: Zauwa ga Alhaji/Hajiya, Ka/ki, kai/ku da sauransu.
  11. Babu wata doka da ta yanke hukuncin matsayin harafin da zai biyo bayanta. Yana iya zama babba ko ƙarami.

  12.  Alhamza (‘): Ana ɗiga wannan alama a tsakanin harrufa a cikin kalma ɗaya domin samar da cikakkiyar ma’ana. Dokar da za a kiyaye ita ce, cewa, ba a ɗiga ta a tsakanin tagwayen baƙaƙe (gw, sh, ky da sauransu). Misalanta sun haɗa da:
    • Mariya ‘yar’uwar Kande ce.
    • Anya kuwa wannan maganar da yake faɗa tana da ma’ana?

A taƙaice waɗannan su ne alamomin rubutun da za mu iya kawowa a wannan darasin. Idan mai karatu ya bisu daki-daki tare da kaifafa tunani, zai fahimci cewa suna taimakawa matuƙa wajen sauƙaƙa wa mai karatu karanta rubutu da fahimtarsa.

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub