Barkwanci

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Barkwanci


Gabatarwa

Barkwanci maganganu ne da ake yi a tsakanin mutane da nufin ban dariya. Ana yin barkwanci ne ta hanyar ba’a. Hakanan kuma ana iya kallonsa a matsayin wasan ban dariya, saboda zamowarsa maganganun da ake yi ta cikin raha, da wasa kuma ana dariya. Komai ɗacin kalmar da aka faɗa, bata ɓata rai sai dai a yi dariya. Misali, wasan tsakanin ƙabila da ƙabila, Babarbare (Kanuri), yakan ce da Bafullace biri, ko ɓarawo, shi kuma Bafillace yakan mayar da martani. To, amma maimakon rai ya ɓaci, sai dai ka ga ana dariya. Ko kuma ka ji Bakano yana ce da Bazazzagi kwarto. Sukan ce Zariya ba ɓarawo idan ka ji ihu kwarto ne.

Fa’idojin Barkwanci

Akwai fa’idoji masu tarin yawa tattare da barkwanci:
  1. Nishaɗantarwa: Akwai nishaɗi a cikin barkwanci, kasancewarsa wasa da ake yi ta hanyar magana kuma a saka juna dariya. Ita kuwa dariya, hanya ce mai matuƙar muhimmanci ta saka nishaɗi.
  2. Ƙara Danƙon Zumunci: Barkwanci yana ƙarfafa zumunci tsakanin masu yinsa. Ana kawar da gaba ta hanyar barkwanci. Misali, barkwanci tsakanin ƙabilun da suka yaƙi juna ko kuma masu sana’o’in da kusan suke kishiyantar juna, misali a ce mahauci da masunci. Sukan cirewa junansu ƙyashi ta hanyar barkwanci.
  3. Ilimantarwa: Akwai ilimatarwa a cikin barkwanci, saboda ta hanyar barkwanci ake ƙirƙiro wasu gajerun labarurrukan da ake raɓa su da wata ƙabilar wanda a cikin irin waɗannan labaru za a ga akwai hikimomin da za a samu ilimin rayuwa a ciki. Misali, Barebari suna cewa wai wani Bafullace ne mota ta kaɗe shi har ya fita hayyacinsa ta inda har aka kai shi asibiti bai sani ba. To bayan ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya yi, sai ya ga likita cikin fararen kaya yana tsaye a kansa, shi kuma bafullacen yana kwance kan gado, ga katifa mai laushi, ga kuma fanka tana firfita shi da sauran kayan alatu. To wai da likita ya tambaye shi sunansa sai ya ce, “Da dai a duniya ana she min Ja’o, amma yanzu Nawakiri (Walakiri) sai abin da ka she (ka ce)”.
Idan muka lura da wannan gajeren labari, za mu ga akwai karantarwa dangane da daɗin da ke lahira a cikinsa.

Rabe-Raben Barkwanci

Ana iya karkasa barkwanci bisa la’akari da masu yinsa. Za mu iya samun rabe-rabe kamar haka:
  1. Barkwancin Zumunta: Shi ne barkwancin da ake yi tsakanin ‘yan’uwa ko dangi, da sauran makamantansu. Akan yi wannan barkwanci tsakanin kaka da jika, ‘ya’yan wa da na ƙani; wato tsakanin mutanen da suka haɗa kakanni guda koda kuwa kaka ɗaya suka haɗa. Sannan kuma akwai barkwanci tsakanin matar wa da matar ƙani, da kuma tsakanin matar wa da ƙannen mijinta, da sauran makamantansu.
  2. Barkwancin Ƙabila: Ana barkwanci tsakanin wata ƙabilar da wata. Wannan barkwanci ne da ake ganin faruwar yaƙi tsakanin waɗannan ƙabilu biyu ko kuma kasancewarsu a gurin zama guda, su ke haifar da shi, dan barkwancin ya kore afkuwar gaba a tsakanin waɗannan ƙabilu.

    Daga cikin irin wannan barkwanci akwai shi tsakanin Barebari da Fulani, Tsakanin Nufawa da Katsinawa, tsakanin Yarbawa da Gobirawa, da sauransu duk a cikin Najeriya.

  3. Barkwancin Sana’a: Shi ne barkwancin da masu sana’ar da ke kishiyantar juna ke yi. Ta hanyar wannan barkwanci ake gusar da ƙyashin da ke tsakanin masu irin waɗannan sana’o’i. misali, akwai barkwanci tsakanin mahauta da masunta, tsakanin maƙera da wanzamai, da sauransu.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub