Kaho

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙaho


Gabatarwa

Ƙaho, abin busa ne da ake busa shi da baki. An fara busa ƙaho a Kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa.


Ƙaho

Mafarauta da ‘yan tauri su ake busawa ƙaho da nufin zaburantar da su domin samun ƙarin ƙarfin zuciya a lokacin gudanar da farauta a daji ko kuma a lokutan bukukuwan da suka shafe su.


Ƙaho, bakin busa

Haka nan ana amfani da ƙaho wajen sanar da mafarauta shirin tafiya daji domin farauta ko kuma su fito daga gida domin gudanar da ayyukan gayya.


Ƙaho, zizito (ƙofar da aka ƙayata da noti)

Ƙaho kala biyu ne: Ƙyaro da kuma Randa. Abin da ke bambanta su kawai shi ne faɗin babban baki; bakin Randa ya fi na ƙyaro faɗi.

Ana samun ƙaho daga dabbobin da suka haɗa da shanu, manyan raguna, ɓauna da sauran su.


Ƙaho, ƙaramin baki

Ana yin ƙaho ne ta hanyar fafe tsininsa a yi masa ƙaramar ƙofa, sannan kuma daga samansa a yi masa wata ƙofar da ake saka baki a cikinta ana busawa. Sai kuma wata ƙaramar ƙofa da ake yi daf da babban bakin ƙaho wadda ake ce da ita zizito, ita ce ke fitar da sauti.


Ƙaho, babban baki

Ana busa ƙaho ta hanyar riƙe shi da hannaye biyu sannan a ɗora bakin busa a cikin baki, sai kuma babban ɗan yatsa da ake rufe ƙaramin bakin ƙaho da shi. Shi kuma babban bakin ƙaho ana rufe shi da tafin hannu kamar yadda Omo mai busa ƙaho ya shaida mana a cikin tattaunawar da muka yi da shi a ranar 7/6/2019 a gidansa da ke Jalingon Jahar Taraba.


Omo yana busa ƙaho

Kalli Yadda Ake Busa Ƙaho

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Gusau S. M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Northern Nigerian Publishing Company. (1970). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company, Zariya – Najeriya.

Tattaunawa da Omo Mai Ƙaho, a ranar 7/6/2019 a gidansa da ke garin Jalingo, Jahar Taraba a Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub