Camfi a Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Camfi a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Camfi, hanya ce ta zato da Bahaushe ya gina kansa a kan ta dangane da faruwar wasu abubuwa. Wannan al’ada ta camfi, na daga cikin munanan al’adun da Bahaushe ya ke da su tun dauri. Bahaushe yana aƙidantuwa da zace-zace da ya yi dangane da faruwa ko afkuwar wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa. Wannan al’ada masana suna yi mata kallon mummunar al’ada ce.

Ma’anar Camfi

A al’adance idan aka ce camfi ana nufin, ƙudurcewa da mutum ya ke yi a zuciyarsa cewa idan ya aikata wani aiki, ko ya faɗi wata magana, ko wani abu ya faru da shi, to sakamakon faruwar wannan abun, wani abu kuma daban, wanda ka iya zama kakkyawa ko akasin haka na iya faruwa da shi.

Amma Farfesa Ɗangambo (1984), cewa ya yi, “Camfi, shi ne, mutum ya ɗauka cewa, in ya yi wani abu, ko ya ce wani abu, ko ya ji wani abu, to, ya gaskata wani abun zai faru, sakamakon haka.”

Su kuwa Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), cewa suka yi, “Wata hanya ce ta ƙudurce aukuwa ko faruwar wani abu da sakamakonsa zai iya zama mai kyau ko mai alheri ko mai muni.”

Kenan, bisa la’akari da waɗannan maganganu na masa game da ma’anar camfi, za a iya fahimtar cewa, camfi ƙuduri ne da ake gina shi a kan zato. Saboda, za to ne ake yi cewa idan aka yi wani abu, ko aka faɗi wani abu, da sauran su, to wani abu na iya faruwa. Babu tabbas cikin faruwar wannan abun.

Misalan Camfe-Camfe

A misalce, Bahaushe ya ƙudurce cewa;
  • Idan mutum ya zauna a ƙofar ɗaki, aljanu suna iya bugunsa.
  • Idan mutum ya ji hannunsa na dama yana ƙaiƙayi, zai samu arziƙi.
  • Idan mutum ya taka kashi da safe, zai samu arziƙi a wannan rana.
  • Idan mutum ya ji ƙafarsa tana ƙaiƙai, to zai yi tafiya.

Ke nan, idan aka lura da waɗannan ƙudurori da suka zo a matsayin misalsalin camfe-camfe, za a fahimci cewa zato ne kawai. Don haka wannan al’ada ba ta da kyau. Kuma masana sun yi gargaɗi da a nuisance ta.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub