Tsarin Sauti: Furucin Baƙaƙe

Me ka ke nema?


Tsarin Sauti: Furucin Baƙaƙe


Gabatarwa

A fannin nazarin sautin Hausa, baƙi, shi ne “Ƙwayar sautin da wajen furta ta wasu sassa na bakin mutum kan taɓa juna ko kuma su matsi juna”, kamar yadda ya zo a Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010).

Furuci kuma shi ne sautin da ya fito daga bakin mutum, wanda yake samuwa sakamakon aikin gaɓoɓin sauti ko furuci da kuma gaurayar iska, wacce su gaɓoɓin ke tarewa ko kuma su matse ta ta rasa isasshiyar hanyar fita. Saboda haka a fagen nazarin sauti, ana nazartar furucin baƙaƙe ta fuskoki uku: Muhalli ko gurin furuci; yanayin furuci da kuma matsayin maƙwallato a yayin furuci.

Manazarta:


Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M (Babu Shekara). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Nigeria.

Sani M.A.Z. (2007). Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Sani M.A.Z., Muhammad A. Da Rabeh B. (2000). Exam Focus Hausa Langugae Don Masu Rubuta Jarabawar WASC da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M da ‘Yar’aduwa T.M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Zarruƙ R., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub