Hausa Gatse

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Gatse


Gabatarwa

Gatse, salon magana ce da ke cike da tarin fasaha wajen iya zance. Magana ce wacce duk abin da aka faɗa ba shi ake nufi ba. Wato salon magana ce da e ta ke zuwa a matsayin a’a, yi, ta ke zuwa a matsayin kar a yi. Wato dukkan abin da aka faɗa ba shi ake nufi ba, akasin sa ake nufi.

Babu wani takamaiman lokaci ko wuri ko wasu mutane da suka keɓanta da yin gatse. Amma an fi yinsa ko dai a lokacin da mutum yake fushi ko kuma yake kusa da yin fushin. Misali, idan aka ce da mutum ya aikata wani aiki mummuna, wanda shi kuma yana ganin kamar sa a ce ya aikata wannan aikin, ya wuce nan. To, idan aka ce wane kai ka aikata ka za? Sai shi kuma ya ce e, ni ɗin ne. A wannan gaɓar za a gane cewa gatse yake yi idan aka lura da yanayin fuskarsa da kuma sigar da ya faɗi maganar. Saboda duk lokacin da za a yi gatse, da wahala a ga fuskar mai yin gatsen ba a ɗaure ba. Sannan kuma sigar fitar maganar ita ma za a ga da alamar zafi a ciki.

Sannan kuma a wasu lokutan da yara kan tambayi izinin aikata wani aikin da bai kamata ba, akan yi musu gatse. To ko a nan ɗin ma jin haushin tambayar shi ke saka wa a yi gatsen. Misali, kamar a ce an kawo wani abin amfani a gida da ya kamata a ce kowa a gidan ya samu wani adadi, to wani daga cikin yara bayan ya ɗauki nasa sai kuma ya ce na ƙara wani? Sai a ce da shi e, ƙara mu gani.

Haka nan a wasu lokutan akan bibiyi gatse da ƙwafa, gyaɗa kai, cizon fatar baki, harara, da sauran su. Duk waɗannan idan suka biyo bayan magana suna tabbatar da cewa wannan magana gatse ce.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub