Hausa Habaici

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Habaici


Gabatarwa

Habaici salon magana ne da Bahaushe ke amfani da shi wajen isar da wani saƙo a hikimance ta cikin zance. Wannan saƙon zai iya kasancewa gargaɗi, huce haushi, jan-kunne da sauransu. Magana ce da ake yin ta a cikin duhu; ma’ana, ba kai tsaye ake fito da maganar ba, sai dai shi wanda ake yi dominsa ya san inda aka dosa. Ko kuma idan abin ya shafi wani laifi ne da mutumin ya aikata, to duk wanda ya san ya aikata laifin shi ma zai iya sanin inda aka dosa. Amma in ba haka ba, sanin inda aka dosa cikin habaici yana da wahala.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), su ka ce, “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum”.

Dalilan da suke sa yin habaici suna da yawa, daga ciki akwai tsokanar faɗa, jan-kunne, gargaɗi, ramuwa, kishi, ƙyashi, hassada, rowa, aikata wani abin ƙi, da sauransu. Kowane ɗaya daga cikin waɗannan dalilai da aka zayyana da ma wasunsu, in suka faru sai a yi amfani da habaici a cusa wa wanda ake magana da shi haushi. Shi kuma Farfesa Ɗangambo (1984) cewa ya yi, "Habaici, wata hanya ce ta zagin mutum a fakaice".

Hanyoyin da ake bi wajen yin habaici akwai gugar zana, karin magana, harbin iska, da sauransu. Misali:

  1. Idan wani ya shiga sabgar wani a wani lokaci, yana iya bari sai daga baya ya ce, daga yau in mutum ya ƙara shiga sabgata, sai na turmumusa hancinsa a ƙasa. Ka ga wannan jan-kunne ake yi amma ta cikin habaici. Maimakon a ce wane daga yau in ka ƙara shiga sabgata zan yi maka kaza. Ko kuma a ce, wane, daga yau hawainiyarka ta kiyayi rama ta. A nan kuma an yi habaici ne mai kama da karin magana.
  2. Idan wani ya sayi wani abu kamar abun hawa haka, ana iya bayyana hassadar da ake yi masa ta cikin habaici. Misali, a ce, mu ma dai mun kusa sayen motar nan. Za a gane cewa hassada ce idan aka lura da cewa a nan mai faɗin maganar maimaikon ya taya wanda ya sayi motar murna sai ya ɓuge da cewa shi ma dai zai saya.
  3. Idan wani ya nuna son ya mallaki wani abu, za a iya cewa da shi, nan gani, nan bari. Ko kuma a ce ƙwalele dokin Iliya, ba ni sayar da kai, ba ni ba da aron ka. Da sauransu.

Akwai dangantaka tsakanin habaici da zambo, saboda zamowarsu duk zagi ne da ake yi wa mutum ba tare da kama suna ba. Sai dai shi zambo yakan fito da siffar wanda ake zagi ta yadda kowa zai iya gane shi.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub