Rumbun Ilimi - Ƙa’idojin Haɗe Kalma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙa'idojin Haɗe Kalma


Gabatarwa

A dokokin rubutun Hausa, akwai wasu kalmomin da ba a raba su, a haɗe ake rubuta su. Daga cikinsu akwai:

  1. Zagin aikatau.
  2. Kalmomin jama’u.
  3. Kalmomin nuni.
  4. Kalomin tambaya.
  5. Wajen rubuta sunaye.

Zagin Aikatau

Kalmomi ne da suke nuni ga wani aiki da aka saba aikatawa. Farfesa Bunza (2002), ya kira su da “Sababben Lokaci”. Waɗannan kalmomi gaurayayyu ne, ana gauraya wakilin suna ne da bigire na “Kan”, ko “ke” sai a samar da su. Duba waɗannan misalan:

  1. Idan ya ta haɗu da  kan, sai su zama yakan.
  2. Idan su ta haɗu da kan, sai su zama sukan.
  3. Idan ta ta haɗu da kan, sai su zama sukan.
  4. Idan mu ta haɗu da kan, sai su zama mukan.

Dukkan waɗannan zagagen aikatau ko sababben lokaci a haɗe ake rubuta su a dokar rubutun Hausa. ga misalai a cikin jimla:

  1. Da’u fataken dare, da rana suke barci.
  2. Yakan sayi ƙosai da safe.
  3. Ni nakan sayar da littafin Ahlari.
  4. Bala da Binta sukan tafi makaranta tare.
  5. Akan dafa zogale a ci.

Kalmomin Jama’u

Kalmomi irin su kowane, kowanne, kowacce, kowace, koyaushe, da kowaɗanne, a haɗe ake rubuta su a bisa dokar rubutun Hausa. Misali:

  1. Kowane mutum, ya riƙa tuna Ubangijinsa.
  2. Kowanne gari yana da sarki.
  3. Kowacce rana, kasuwa ce.
  4. Kowace mace, ya kamata ta zama matar kirki.
  5. A riƙa faɗin gaskiya a koyaushe.
  6. Kowaɗanne riguna akwai yadda ake wanke su.

Kalmomin Nuni

Kalmomi irinsu wannan, wancan, waɗannan da waɗancan, dokar rubutun Hausa ta ce a riƙa rubuta su a haɗe. Misali:

  1. Wannan littafin yana da nagarta.
  2. Wancan littafin ba shi da nagarta.
  3. Waɗannan yaran suna da ƙoƙari.
  4. Waɗancan yaran basu da ƙoƙari.

Kalmomin Tambaya

Kalmomin tambaya su ne, wane? Wacce? Mene? Waɗanne? Dokar rubutun Hausa ta ce kar a raba su idan aka zo rubutawa. Misali:

  1. Wane ne yake magana?
  2. Wace ce ta gaya maka?
  3. Mene ne abin wahala a ciki?
  4. Waɗanne darrusa ka fi so a Rumbun Ilimi?

Wajen Rubuta Sunaye

Farfesa Bunza (2002), ya jero ire-iren waɗannan sunaye ya ce, dokar rubutun Hausa ta ce a riƙa haɗe su kar a raba su. Daga cikin irin waɗannan sunaye akwai:

Alƙur’ani, Almasihu, Ɗanlami, Alhaji, Abdulaziz, Nakowa, Attaura, Linjila da sauransu. Sai kuma a faɗaɗa.

Yanzu kenan a taƙaice mun fahimci cewa, dokar rubutun Hausa ta samar da wasu ƙa’idoji da ake son kiyayewa idan aka zo yin rubutu, cewa a akwai wasu kalmomi da ake haɗe su a rubutu. Daga ciki mun ga cewa zagin aikatau ko sababben lokaci, kalmomin jama’u, kalmomin tambaya, kalmomin nuni da sunayen mutane da sauransu, duk haɗe su ake yi idan aka zo rubutu.

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub