Hikaya: Jemage

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Jemage

Gabatarwa

Jemage wata halitta ce mai kama da tsuntsu. Yana rayuwa rataye a sama, wanda ka iya zama jikin reshen bishiya, ƙoƙuwar ɗaki, jikin ciyawa, dirkar ɗaki, da sauran dangogin su.

Ta fuskacin halittar jiki kuwa, jemage yana da fukafukai haɗaɗɗu guda biyu marasa gashi da kuma tsaga. Fukafukan nasa na fata ne kuma fatar mai kauri ce ga kuma taushi. Da waɗannan fukafukai na fata ya ke rufe dukkan jikinsa. Yana da wasu farata zaƙo-zaƙo masu tsini a jikin yatsun ƙafarsa. Waɗannan faratu da su yake maƙalƙale reshe da sauran su ya ɗafe a jiki ya yi barci. Fuskarsa kuwa irin ta kyarkeci ce. Yana kuma da faka-fakan kunnuwa da suke taimaka masa wajen jin sauti komai ƙanƙantar sa.

Jemage, haihuwa ya ke yi, ya kuma shayar da 'ya'yansa nono kamar dabba, wanda wannan abu ne ba sabun ba a wajen tsuntsaye. Yana kuma tashi sama, wannan kuma abu ne da ya gagari dabba. Saboda wannan sassaɓawa tasa tsakanin dabbobi da tsuntsaye, sai ake yi masa kirari da, jemage, kai ba tsuntsu ba sannan ba dabba ba.

Jemage, yana cin abincin da ya haɗa da ƙananan ciyayi, ƙanan ƙwari, 'ya'yan itatuwa, da sauran su. Duk karakainar da jemage ya ke yi, da dare ya ke yi, idan kuwa aka gan shi da rana, to za a ga yana karo da katangun gidaje da kuma bishiyoyi. Wannan kuma saboda zamowar idanuwansa basa gani da rana. Wannan shi ne jemage, shi ba tsuntsu ba, sannan kuma ba dabba ba.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub