Hikaya: Mujiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hikaya: Mujiya


Gabatarwa

Ke mujiya, wasa na rana ba naki ba…

Mujiya, ɗaya ce daga cikin tsuntsaye, tana da matsakaicin girma da kuma manyan idanuwa. Sai dai, duk da waɗannan manyan idanuwa nata, ba ta gani da rana.

Wata rana, Buba da ƙaninsa Da'u suka fita yawo, suna cikin tafiya a cikin gonaki, sai Da'u ya hangi wasu ƙanan kurace sun yayyaɓe mujiya suna ta kai mata bara. Sai Da'u ya tsaya cikin mamaki, ya tambayi yayansa ya ce da shi, ka ga wani ikon Allah, ga wasu ƙananan tsuntsaye sun kewaye mujiya sun hana ta sakat.

Da Buba ya kalli saman mangwaro, sai ya hangi mujiya a tsakiyar tsuntsaye sun kewaye ta. Saboda haka sai ya yi wa Da'u bayani da cewa, wancan babban tsuntsun mujiya ce, ya ci gaba da gaya masa cewa, ai suna ɗaukar fansa ne, saboda takan kama su da dare ta kashe ta ci. Ita kuma bata gani da rana, saboda hasken rana yana hana ta gani. Saboda haka babu jituwa tsakanin ta da sauran tsuntsaye da ma wasu ƙwari kamar irin su ƙadangare, ɓera, bushiya, da sauran su. Tana kuma da wani irin kuka da ta ke yi da dare, duk wanda ya ji kukan ta a cikin su da dare, maɓoya ya ke nema. Amma yanzu suna iya yi mata komai, kasantuwar ba ta gani da rana.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub