Kukuma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kukuma


Gabatarwa

Kukuma tana ɗaya daga cikin kyana kiɗan Hausa wacce ta ke a rukunin kayan izga. Makaɗa gama-gari su suke kaɗa kukuma ga abubuwa ko mutanen da suka ɗauki hankalinsu ko kuma wanda ya gayyace su a lokutan bukukuwan Hausa da suka haɗa da aure, suna da sauran su.


Kukuma

Ana haɗa kukuma da kayayyakin da suka haɗa da:

 1. Ƙoƙo.
 2. Yazga/Izga: Ita ce gashin jelar doki.
 3. Itace: Shi ne itacen marke ko kuma duk wanda ya samu. Wanda ake samu a sassaƙa shi gwargwadon buƙata.
 4. Zaren Kaɗi: Zare ne wanda mata suke kaɗa shi, wanda ake amfani da shi a masaƙar gargajiyar Hausa. Yanzu kuwa, da na zamani ake amfani.
 5. Fatar Guza.
 6. Ƙayar Aduwa.
 7. Itacen Lalle: Da shi ake yin jakin kukuma.
 8. Anini.

Baka

Itace ne ƙarami ake yi masa sha irin na baka a ɗaura tsirkiya a jikinsa. Ana ana haɗa ta da:

 1. Itace.
 2. Yazga.
 3. Wuri.


Bakar Kukuma

Yadda Ake Haɗa Kukuma

Za a samu ƙoƙo a fafe cikinsa sannan a yi masa ƙofa a sama a rufe ƙofar da fatar guza. A saman fatar sai a yi ƙofofin da za su riƙa fitar da amo. Sannan kuma sai a yi wasu ƙofofin guda biyu a gefen ƙoƙo waɗanda za a zura sandar kukumar a ciki. Sai kuma a ɗaura yazga daga saman sandar ta biyo ta kan fatar da aka rufa a kan ƙoƙon sannan a kai ta ƙasan a ɗaure a jikin sandar da ta fito ta cikin ƙoƙon.

Yadda Ake KHaɗa Kukuma


Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Alhaji Muhammadu Takafalla. Wazirin Garba Sufa Mazaunin Garin Jogana, Jahar Kano, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub