Kalangu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kalangu


Gabatarwa

Kalangu, kalma ce da ake amfani da ita a Hausa, wajen ambato wata nau’in ganga da makaɗa ke amfani da ita wajen yin kaɗe-kaɗe da dama. Idan aka zo wajen kiɗan kalangu, ana haɗa kayan kiɗa kusan guda huɗu.


Kayan Kiɗan Kalangu

Akan kaɗa ita gangar Kalangu ita kaɗai a wasu lokuta, kamar kiɗan nama; wanda kiɗa ne da ake yin sa idan aka yanka wata babbar dabba kamar Saniya musamman a ranakun kasuwar gari.

Bayan zamowar kiɗan kalangu kiɗa mai zaman kansa, akan kuma gauraya shi a cikin wasu kayan kiɗan domin samun mabambantan amo da dama. Misali, ana haɗa shi da gurmi, kukuma, da sauransu.

Ma’anar Kalangu

Kalangu, ganga ce da ake sassaƙa ta daga icen bishiyar ƙirya ko alulluba. Ana sassaƙa icen ya tafi baki ɗaya da girma da kauri gwargwadon tsawon da ake so. Sannan kuma sai a fafe/rarake cikin, ya zama an samar da kwararo. Sai kuma a sake sassaƙe bayan, a bauɗar da tsakiyar a yi masa wani irin sha. Daga sama ta kowane gefe yana da faɗinsa, amma a tsakiya kuma ya matse. Sannan sai a rufe bakunan da fata. Sai kuma a kawo tsirkiya a zazzarga daga gefe zuwa gefe. Kalangu kenan.


Kalangu

Kayan Haɗin Kalangu

  1. Icen Ƙirya ko Alulluba
  2. Fatar akuya ko ta ɗan tayin akuya
  3. Tsirkiya: Jemammiyar fata ce da ake yayyanka ta ana yin igiya da ita. da ita ake ɗame kalangu ana rufe shi.
  4. Saƙe: Saƙaƙƙen zare ne da masaƙa ke saƙawa. Da shi ake yin maratayi.

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub