Kanzagi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kanzagi


Gabatarwa

Kanzagi ganga ce ƙarama. Komai nasa irin ɗaya ne da na kalangu. Abin da ya bambanta su shi ne girma. Kalangu ya fi kanzagi girma. Amma yadda ake kaɗa su, da kayan da ake kaɗa su duk irin ɗaya ne.

Shi kanzagi ɗan agaji ne, tare ake kaɗa su da kalangu. Mun gani a shafin kalangu cewa ana iya kaɗa shi kaɗai a wasu lokutan. Amma shi kanzagi baya kaɗuwa shi kaɗai. Koda an kaɗa shi shi kaɗai, kiɗan ba zai yi ma’ana ba.

Babbar gudunmawar da ya ke bayarwa a kayan kiɗan kalangu ita ce, ƙara zaƙin amo.


Kanzagi

Kayan Haɗin Kanzagi

  1. Icen Ƙirya ko Alulluba
  2. Fatar akuya ko ɗan tayin akuya
  3. Tsirkiya: Jemammiyar fata ce da ake yayyanka ta ana yin igiya da ita. da ita ake ɗame kalangu ana rufe shi.
  4. Saƙe: Saƙaƙƙen zare ne da masaƙa ke saƙawa. Da shi ake yin maratayi.

Manazarta:


Gusau S.M. (2017). Kayan Kiɗan Hausa. Centuary Research and Publications, Kano – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.  

Tattaunawa da Umaru mai gurmi a garin Uke ta jahar Nassarawa a ranar Alhamis 14/3/2018.

Tattaunawa da Sarkin Kiɗan garin Alitini, Isma'ila Namarke, a garin Alitini, ƙaramar hukumar Warawa, a Jahar Kano, Najeriya. A ranar 17 ga watan 6, na shekarar 2017.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub