Hausa Ƙarangiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Ƙarangiya


Gabatarwa

Ƙarangiya salon magana ce ta hikima wacce ake yi don nuna gwanintar harshe ko koyar da yara yadda za su iya magana. Akan kuma kira wannan salon magana da Kakkarya Harshe ko Gagara Gwari.

Masana fannin Hausa sun bata fassara gwargwadon hali. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce, “hikima ce ta sarrafa harshe, domin koya wa yara iya magana”. Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), suka ce, “salon sarrafa sautuka ta cuɗanya muryoyin kalmomi su rinƙa maimaita junansu cikin taƙidi don nuna gwaninta”.

Amfanin Ƙarangiya

Haƙiƙa akwai abubuwan amfani a cikin wannan salo na magana:
  1. Yana karantar da yara ƙwarancewa wajen sarrafa harshe.
  2. Yana ƙara wa yara kaifin tunani da natsuwa, saboda su kalmomin da ake furta wa suna da kamanceceniya, sannan kuma da sauri da sauri ake son faɗin su. Saboda haka idan ba a yi a hankali ba sai ya zama a wasu lokutan mutum ya tsinci kansa wajen furta kamlomin da basu da ce ba.
  3. Nishaɗantarwa, akan samu nishaɗi cikin ƙarangiya musamman idan aka samu wanda ya kasa faɗi sai sautin ya koma wani iri wanda wannan kan saka shi mai yin da masu sauroro su yi dariya.

Rabe-Raben Ƙarangiya

An rarraba su bisa la’akari da yadda ake yin su:
  1. Gagara Gwari: Shi ne matakin farko na salon maganar ƙarangiya wacce ake koya wa yara a makaranta. Saboda haka yara ma na iya yin wannan. Amma wani wanda ba Hausa ce yarensa ba, sannan kuma ba a cikin Hausawa aka haife shi ba, to, faɗin su daidai zai zama da kamar wuya, gurguwa da auren nesa, a gare shi. Misali:

Kai jan mutumin nan,
Ka ɗauki jar sandar can,
Ka kori jar akuyar can,
Mai cin jar dawar can,
Ta gaba da gonar Jatau.

  1. In giza bami: Salon magana ne da ka iya ingiza wanda ba shi da lura ya wayi gari yana faɗin maganar batsa ko ma zagi a wasu lokutan. Saboda haka samari da ‘yan mata su suka fi amfani da irin waɗannan. Misali, Na bugi bakin dokin baba da bayan hannu. A nan da zarar kalmar dokin ta zame, sai a wayi gari ana faɗin “Na bugi bakin baba da bayan hannu”. Kenan, an in giza bami ya faɗi magana maras daɗi game da mahafinsa.
  2. Mai Nuna Gwaninta: Turƙashi! Wani kaya sai amale. Shi wannan nau’in salon ƙaraginya sai gwanaye a Harshen Hausa suke iya yinsa. Mawaƙa su suka fi yin wannan dan nuna gwanancewarsu a harshe.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Yahaya I. Y. (1971). Tatsuniyoyi da Wasanni, Littafi Na Ɗaya. Oxford University Press.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub