Rumbun Ilimi - Karin Magana

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana


Gabatarwa

Karin magana salo ne na yin magana taƙaitacciya kuma dunƙulalliya wacce ke ɗauke da ma’ana mai faɗi dan isar da saƙo ta cikin hikima. Akan yi amfani da wannan salo wajen yin nuni, gargaɗi, yabo, ƙarfafa guiwa, da sauransu duk a hikimance, ta yadda kusan in ba cikakken Bahaushe ba, fahimar wannan zance yana da wahala.

Ma’anar Karin Magana

Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai:
Farfesa Ɗangambo (1984) da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan, cikin hikima”.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992) , “Karin Magana Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai faɗi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki”.

Kenan idan aka lura sosai, za a ga cewa ita karin magana, magana ce dunƙulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shuɗe, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abinsa. Misali, ana iya yiwa mutumin da bashi da tattali nuni cikin ‘yan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da ka ke yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da kuma maras amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu maras daɗi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da ɗa, mai ido ba. Da sauransu.

Kowace ɗaya aka ɗauka daga cikin waɗannan karin magana guda biyu, za a taras cewa maganganu ne dunƙulallu, waɗanda idan aka tashi farfasa su, za su ci guri mai yawa. Amma idan aka faɗe su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru, sannan kuma shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi.

Amfanin Karin Magana

  1. Taƙaita doguwar magana.
  2. Nuni, gargaɗi, da faɗakarwa cikin nishaɗi, sannan kuma a taƙaice.
  3. Bayyanar da ƙwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.
  4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana ƙarawa zance kyau da kuma daɗi.

Gaba Karin Magana I

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub