Karin Magana IV

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana IV


  1. A cikin ido, ake tsawirya.
  2. A yarda ƙullon mangwaro, a huta da ƙuda.
  3. Abin da ya ci doma, ba zai bar awai ba.
  4. Abin da yawa, mutuwa ta je kasuwa.
  5. Abin kasuwa, na mai ciniki ne.
  6. Akuya, bata gasa da kura.
  7. Albarkacin kaza, ƙadangare ka sha ruwan kasko.
  8. Ashe ana tsoron inna? In ji 'ya'yan mayya.
  9. Ba a fafe gora, ranar tafiya.
  10. Ba a haɗa gudu, da susar ɗuwawu.
  11. Ba ka cin rama, sai 'yaryaɗi.
  12. Bakin rijiya, ba wajen wasan makaho ba ne.
  13. Bakina, ƙanin ƙafata.
  14. Bani in baka, shi ne tanka.
  15. Banza girman mahaukaci, ƙaramin mai wayo ya fi shi.
  16. Banza, ta kori wofi.
  17. Baya, ba zane.
  18. Bikin Magaji, baya hana na Magajiya.
  19. Biyu, tafi ɗaya ko a rabon ɗauki.
  20. Ci naka in ci nawa, ba rowa ba ce.
  21. Ciki, mai manta kyautar jiya.
  22. Da baƙo da tukura, duk umbutawa ne.
  23. Da haihuwar yuyuyu, gwara/gara/ƙwara ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara.
  24. Da me, kurna ta fi magarya?
  25. Da muguwar rawa, gwanda/gwamma ƙin tashi.
  26. Dole ne, cin kasuwa da maƙiyi.
  27. Duba mini hanya, makaho ya so tsegumi.
  28. Farar aniya, laya.
  29. Gajen haƙuri, shi yake kawo me aka shuka.
  30. Garin masoyi, ba shi da nisa.
  31. Ginshiƙin dutse, kowa ya yi karo da kai shi ka faɗi.
  32. Girma da arziƙi, ita ke sa a ja sa da abawa.
  33. Gobe ma, rana ce.
  34. Gwano, baya jin warin jikinsa.
  35. Hadarin ƙasa, maganin mai kabido.
  36. Hanci, bai san daɗin gishiri ba.
  37. Hangen Dala, ba shiga birni ba.
  38. Idan amarya bata hau doki ba, ai ko ba a ɗora mata kaya ba.
  39. Idan mutum ya yi nisa, baya jin kira.
  40. Idan ɗan kaciya bai ci kaza ba, ai ba ya yi bara ba.
  41. Ido ba mudu ba, ya san kima/ƙima.
  42. In dama ta ƙiya, sai a koma hagu.
  43. In ka ji ana raka ni kashi, ba zawayi/zawo ba ne.
  44. In ta bi daga-daga, na ƙurya ka sha kashi.
  45. Ina ruwan bebe da harara.
  46. Inda jahilci ya yi kauci, sakarci ne ya zo zai nuna ilimi.
  47. Jaki, yana dukan taiki.
  48. Jelar raƙumi, ta yi nesa da ƙasa/raɓa.
  49. Jiya, ta fi yau/ Da me, jiya ta fi yau?
  50. Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta.
  51. Kai mai kashe maciji, sai ka yi niyya ka ɗauki sanda.
  52. Kaska raɓi mai jini, ki bar shi da gashi.
  53. Kasuwa, a ka miki/maki dole.
  54. Kasuwa, akwashin Allah.
  55. Kaɗan, mai ban haushi.
  56. Kaza mai 'ya'ya, ita ke gudun shaho/shirwa.
  57. Kazar kwanci, ƙirjinki ya saba da danna.
  58. Kifin fadama, baya gasa da na kogi.
  59. Kowa ya bar gida, gida ya bar shi.
  60. Kowa ya ɗora miya, sai ya nemo abun kaɗi.
  61. Kyawun ɗan ƙwarai, ya gaji ubansa.
  62. Magana, jari ce.
  63. Maganin kar a yi, kar a soma.
  64. Mai zuciya ake gayawa biki, ba mai zani ba.
  65. Mai zuma ya zo, mai maɗi sai ya naɗe tabarmarsa.
  66. Masallacin kura, ba a baiwa kare limanci.
  67. Masallacin kura, mai yawan ƙasusuwa.
  68. Maza, dangin gurjiya sai an fasa akan san bidi.
  69. Meye gamin kifi da kaska?
  70. Na Allah, baya ƙarewa.
  71. Na zangi, moriyarka da nisa.
  72. Na zaune, bai ga gari ba.
  73. Nan gani nan bari, farar tumfafiya.
  74. Ƙadangaren bakin tulu, a karka a kar tulu, a bar ka ka ɓata ruwa.
  75. Ƙarfe duka ƙarfe ne, amma a cikin ƙarafa akwai zinari da azurfa.
  76. Ƙasar kago, ta maida kago ce.
  77. Rigakafi, ya fi magana.
  78. Rumbun ƙasa, a tashi a barka.
  79. Sake reshe, kama ganye.
  80. Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya miƙa kai ya yi kallo.
  81. Shirim, ba inuwa.
  82. Sun fi kusa, Auyo da Haɗeja.
  83. Ta fari, ta rago.
  84. Ta faru ta ƙare, an yiwa mai dami ɗaya sata.
  85. Ta leƙo, ta koma.
  86. Taron na ayya, gayyar banza.
  87. Tashi da wuri, shi kan hana gira toho.
  88. Taura biyu, basa taunuwa a baki ɗaya.
  89. Tsiga tsiyau, kazar matsiyaci.
  90. Tsugunne, bata ƙare ba.
  91. Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farin gashinta.
  92. Wanda bai san Allah ba, sai wuta ta ƙona shi.
  93. Ɗan kuka, mai jawowa uwarsa jifa.
  94. Ɗinyar makaho, ta nuna a hannunsa.
  95. Ya ɓace ɓat, kamar ɓatan dabo.
  96. Yabon kai, jahilci ne.
  97. Yanzu-yanzu, sai Allah.
  98. Yautai mugun tsuntsu, masha miyarka sai ya yi dare.
  99. Yaɗin mage, kowa ya ci ka sai ya yi amai.
  100. Zaman duniya, iyawa ne'.

BayaKarin Magana III   Gaba Karin Magana V


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub