Karin Magana V

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Karin Magana V


  1. 'Yar bori, ba ta kallon bori.
  2. Abincin wani, gubar wani.
  3. Aikin banza, harara a duhu.
  4. Aikin banza, shafa lalle a ɗuwawu.
  5. Aikin banza, tura agwagwa cikin ruwa.
  6. Allah ga mu gare ka, bawan sarki ya rasa doki.
  7. Ba a baki na ba, an ce banten sarki ya jirge.
  8. Ba a hana ma bada rago, fata.
  9. Ba a sake wa tuwo, suna.
  10. Ba don mahauci ba, da mai taro bai ci naman saniya ba.
  11. Bakin Rijiya, ba wajen wasan yara ba ne.
  12. Ban ci kasuwa ba, rumfa bata faɗa min ba.
  13. Ban gane ba, an yi yamma da kare.
  14. Baƙar fura, ana gama ki mai gida na mutuwa.
  15. Bin umarni, waiwayen makaho.
  16. Biri da gatari, hasarar mai gona.
  17. Da alheri, uwar kishiya ta hau kura.
  18. Da kamar wuya, a dafa kaza a jefar.
  19. Da na sani, ƙeya ce.
  20. Da ruwan ciki, ake jan na rijiya.
  21. Domin kifin baɗi, ake wanke tunkunya.
  22. Duk wanda ya ce bai iya kuka ba, uwarsa ce bata mutu ba.
  23. Duk wanda ya ce garinsu da nisa, ba a kama shi ya kuɓu ce ba.
  24. Farilla, tusa a cikin barci.
  25. Farin cikin ɓarawo, ya taras da ƙofa buɗe.
  26. Fuska, ita ke sayar da riga.
  27. Gaɗar giwa, toro ke buga ganga.
  28. Ikon Allah, kare da tallan tsire.
  29. Ina sane, karuwa ta taka matar aure.
  30. Jiya ba yau ba, in ji tsohuwa ta ga kuɗin tsarince.
  31. Jure fari, na mai akuya ne.
  32. Kafin a yi ɗaran, aka yi kwanɗi.
  33. Karambanin akuya, ya saka ta leƙa ɗakin kura.
  34. Kayan amale, ya fi ƙarfin jaki.
  35. Ko biri ya karye, sai ya hau runhu.
  36. Komai baƙin cikin ɗan tsako, ba zai ci ɗan shirwa ba.
  37. Kura-ta-ci-kura.
  38. Kyawun saurayi, ya auri budurwa.
  39. Lange-lange, mai ramar ƙeta.
  40. Mai bunu a gindi, baya kai gudunmawar gobara.
  41. Mai rawar kai, baya ɗigirgire.
  42. Mai tsoron ta mutu, shi yake maho.
  43. Me na sama ya ci, balle ya baiwa na ƙasa.
  44. Me za a fasa? Mutuwa ko hisabi?
  45. Mu je zuwa, mahaukaci ya hau kura.
  46. Mutu ka raba, takalmin kaza.
  47. Naman da ya fi kusa da wuta, shi ya fi saurin gasuwa.
  48. Nesa-nesa, kallon kurar Jatau.
  49. Nono ya sake hali, mage ta sha tinya.
  50. Ƙawancen gaskiya, a yi shi da wando.
  51. Ƙazantar da ba a gani ba, sunanta tsafta.
  52. Ragamar damisa, a jaki da nisa.
  53. Randar cikin ɗaka, Allah ke ba ki ruwa.
  54. Raƙumi uban gararanba, kowa ya sake ka sai ya nemo ka.
  55. Rashin jini, rashin tsagawa.
  56. Rashin mutunci biki ne, kowa ya yi maka ka rama masa.
  57. Rikicin duniya, da mai rai ake yi.
  58. Ruwan kashe gobara, ba zaɓi .
  59. Sabon salo, gemu a kafaɗa.
  60. Sakarci, dukan kura da gwado.
  61. Sakarci, jiran jirgi a tashar mota.
  62. Sakarci, tura agwagwa a ruwa.
  63. Sandar dukan gurgu, yana kallo ake saro ta.
  64. Sani asali, shi saka kare cin alli.
  65. Saniyar da ba ta da jela, Allah ke kore mata ƙuda.
  66. Sara ɗaya, shi ke da bishiya.
  67. Shegen sama, kura tahangi biri.
  68. Tafiya ta tashi, ƙuad ya ga mai tallen tsire.
  69. Tashin hankali, ba a sa maka rana.
  70. Tsautsayin tauna, maye ya ci jariri.
  71. Tsohuwar mota, ga shan mai ga aiki.
  72. Tsugunne ba ta ƙare ba, an sayar da kare an sayi mage.
  73. Tunku, ya san jiɓar da ya ke yi wa kashi.
  74. Tuntuɓe, daɗin gushi.
  75. Turancin ungulu, sai sarkin fawa.
  76. Tusa, ba ta hura wuta.
  77. Umma, umma biyu, ta fi umma ɗaya.
  78. Ungulu, ba kazar kowa ba ce.
  79. Ungulu, ta koma gidanta na tsamiya.
  80. Walbisi, in ji kare da ya taka sisi.
  81. Wanda ba shi da doki, ba ya ƙyamar jaki.
  82. Wanda bai nom aba, ba ya ƙyamar awo.
  83. Wanda ya ci da kansa, shi ne sarkin noma.
  84. Wawa ana sonka, amma ba a son haihuwar ka.
  85. Wawa, dariyarka abin da dariya.
  86. Ɗan agola, mai wuyar ban nama.
  87. Ɗan maciji ya fi ɗan kura tsiya.
  88. Ɗiɗiricin balaga, kiran miji da akaifa.
  89. Yau da gobe karyar Allah, komai gudun mutum ta kamo shi.
  90. Yau da kallo, gobe da labari.
  91. Yawan shekaru, ba shi ne wayo ba.
  92. Zubar da miyau, masomin hauka.
  93. Zubar da yawu, masomin hauka.
  94. Zuma, sai da wuta.

BayaKarin Magana IV   Farko Karin Magana


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub