Hausa Kirari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Hausa Kirari


Gabatarwa

Kirari maganganu ne na kambawa da ake yi wa mutum ko kuma shi ya yi wa kansa. Kirari kan ƙara gwarzanta wanda aka yi wa. Ana amfani da ƙwarewar zance wajen yin kirari.

Akwai dangataka tsakanin kirari da kuma take. Maroƙa su ke kiraranta mutum, su gwarzanta shi, su kambama shi, su zuga shi da sauransu, bayan makaɗa sun kaɗa masa takensa, wannan gaɓa ita ta ƙulla alaƙa tsakanin kirari da kuma take. Sannan bambancin da ke tsakaninsu kuma shi ne cewa shi kirari maganganu ne, take kuma kiɗa ne. Koda an ji maganganu a lokacin da ake kaɗa kirari, za a taras cewa ana bayyana abin da kiɗa ko busa ke faɗa ne domin masu ƙaramin azanci su fahimta.

Akwai ƙwarewar magana da salo-salon sarrafa harshe a cikin kirari. Akan siffanta mutum da wani abu domin a fito da martabar wannan mutumin. Dubi gurin da maroƙin Shata yake siffanta shi da mai maƙogwaron ɗanyen zinare, domin ya nuna tsananin kyawun muryar Shata wajen waƙa. Idan aka saurari wannan kirari, za a ji yadda wannan maroƙi yake ta zuga Shata, yake nuna masa shi wani na daban ne. Haka nan shi kansa Shatan akwai gurin da yake kuranta kansa a cikin Bakandamiyarsa inda yake cewa:

“Allah ya yarda,
Har yau ni ke yi,
Baku samo canji na ba,
Balle in zauna,
Wai har in ce zan huta, in dai ɗan samu in sarara.

A’a, wane hutu Shata,
Ka riƙa dai.
Gwauron giwa mai ban tsoro na Habu Ɗan Ibrahim,
Kyarkeci mai wawar sura ɗan yaro,
Zaki mai zarin ƙarfi ɗan iro”.

Haka nan idan muka saurari waƙar Ɗan’anache ta Lawan, za mu ji gurin da ya ke cewa, “…To ya buge ukku, ya kashe ukku, ga wasu ukku sun gaza motsi...”, sannan kuma a cikin kirarin da yake yi wa wani ɗan dambe mai suna duna ya ke cewa, "Duna bugunka ya ɗara bindiga zafi...", da sauransu.

Babu wani takamaiman rukunin mutane da suka keɓanta da a yi musu kirari, ko kuma suka keɓanta da yin sa. A Ƙasar Hausa ba wai kawai mutane ake yi wa kirari ba, a’a, har ma da sauran halittu da abubuwa marasa rai.

Ana amfani da salon siffanta abin da ake yi wa kirari da irin kirarin da ake son yi masa. Misali, idan ana son fito da jarumtakar mutum ko wani abu, akan kwatanta shi da zaki, giwa, damisa, doki da sauransu, wannan kuma saboda ƙarfin da suke da shi. Idan kuma ana son bayyana irin yawan kyauta da mutum ya ke yi, sai a kwatanta shi da damina,  da sauransu. Mai haƙuri kuma akan kwatanta shi da damo, da sauransu. Haka-haka, abubuwan ke tafiya. Wato idan ana son siffanta mutum da wani abu sai a nemi wata dabbar ko wani abun da ya yi fice da wannan siffar a danganta shi da ita.

Cikin kirari akwai ƙwarewar magana, sarrafa harshe, taskace al’adu, nishaɗantarwa, ilimantarwa, har ma da gargaɗi da sauran ɗimbin darrusa da za a iya koya.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M. (2002). Harshen da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sikandire. Spectrum Books Limited. Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub