Ƙissa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙissa


Gabatarwa

Farfesa Ɗangambo (1984) ya ce, “Ƙissa, labari ne na gaskiya wanda ya shafi wani annabi. Kuma labari ne da yake cikin alƙur’ani Mai Girma. Misali, ƙissar Annabi Yusufu da Zulaihatu. Shi wannan labari ne na yadda ita wannan mace, Zulaihatu matar wani waziri; uban gidan Annabi Yusufu, ta yi ƙoƙarin ta sa Annabi Yusufu ya neme ta. Amma shi ya ƙi”.

Ƙissar Annabi Yusufu

Allah Mai Girma da Ɗaukaka Ya ce: “A lokacin da Yusufu ya ce wa ubansa, ''Ya baba!  Lalle ne ni, na ga taurari goma sha ɗaya, da rana da wata. Na gan su suna masu sujada a gare ni." Ya ce, "Ya ƙaramin ɗana! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani ƙaidi. Lalle ne Shaiɗan ga mutum, haƙiƙa, maƙiyi ne bayyananne. Kuma kamar wannan ne, Ubangijinka Ya ke zaɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar labarai, kuma ya cika ni'imominSa a kanka, kuma a kan gidan Yakuba kamar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabani, Ibrahim da Is'haƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."

Lalle ne, haƙiƙa, ayoyi  sun kasance ga Yusufu da 'yan'uwansa  domin masu tambaya. A lokacin da suka ce, “lalle ne Yusufu da ɗan'uwansa ne mafiya soyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhali kuwa mu jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙiƙa, yana cikin ɓata bayyananniya. Ku kashe Yusufu, ko, kuwa ku jefa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wofinta saboda ku, kuma ku kasance a bayansa mutane salihai”. Wani mai magana daga cikinsu ya ce, "Kada ku kashe Yusufu. Ku jefa shi a cikin duhun rijiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance masu aikatawa ne.''

Suka ce, "Ya babanmu!  Menene a gareka ba ka amince mana ba a kan Yusufu, alhali kuwa lalle ne mu, haƙiƙa, masu nasiha muke ne a gare shi? Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji daɗi, kuma ya yi wasa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, masu tsaro ne." Ya ce, "Lalle ne ni, haƙiƙa, yana ɓata mini rai ku tafi da shi. Kuma ina tsoron kerkeci ya cinye shi, alhali ku kuwa kuna masu shagala daga gare shi." Suka ce, “haƙiƙa, idan kerkeci ya cinye shi, alhali kuwa muna dangin juna, lalle ne mu, a sa'an nan, haƙiƙa, mun zama masu hasara."

To, a lokacin  da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rijiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kana ba su labari game da wannan al'amari nasu, kuma su ba su sani ba."

Kuma suka je wa ubansu da dare suna kuka. Suka ce, "Ya babanmu!  Lalle ne, mun tafi muna tsere, kuma muka bar Yusufu a wurin kayanmu, sai kerkeci ya cinye shi, kuma kai, ba mai amincewa da mu ba ne, kuma ko da mun kasance masu gaskiya!" Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce, "A'a, zukatanku suka ƙawata muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne Wanda ake neman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke sifantawa”.

Kuma wani ayari  ya je, sai suka aika mai neman musu ruwa, sai ya zura gugansa, ya ce, "Ya busharata! Wannan yaro ne." Kuma suka kama shi yana abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatawa. Kuma suka sayar  da shi da 'yan kuɗi kaɗan, dirhamomi ƙidayayyu. Kuma sun kasance, a wurinsa, daga masu isuwa da abu kaɗan. Kuma wanda ya saye shi daga Masar  ya ce wa matarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammanin ya amfane mu, ko kuwa mu riƙe shi ɗa". Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yusufu, a cikin ƙasa, kuma domin Mu sanar da shi daga fassarar labaru, kuma Allah ne Marinjayi a kan al’amarinSa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba.

Kuma a lokacin da ya isa mafi ƙarfinsa, Muka ba shi hukunci da ilmi. Kuma kamar wancan ne Muke saka wa masu kyautatawa. Kuma wadda yake a cikin ɗakinta, ta neme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙofofi, kuma ta ce, "Ya rage a gare ka!" Ya ce, ina neman tsarin Allah! Lalle Shi ne Ubangijina. Ya kyautata mazaunina. Lalle ne shi, masu zalunci ba su cin nasara!" Kuma lalle ne, ta himmantu da shi. Kuma ya himmantu da ita in ba domin ya ga dalilin Ubangijinsa ba. Kamar haka dai, domin Mu karkatar da mummunan aiki da alfasha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bayinMu salihai yake.

Kuma suka yi tsere  zuwa ga ƙofa. Sai ta tsage rigarsa daga baya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙofar. Ta ce, "Mene ne sakamakon wanda ya yi nufin cuta game da iyalinka? Face a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azaba mai raɗaɗi". Ya ce, "Ita ce ta neme ni a kaina." Kuma wani mai shaida daga mutanenta ya bayar da shaida:  "Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, ta yi gaskiya, kuma shi ne daga maƙaryata. Kuma idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga baya, to, ta yi ƙarya, kuma shi ne daga masu gaskiya".

Sa'an nan a lokacin da ya ga rigarsa an tsage ta daga baya, ya ce, "Lalle ne shi, daga kaidinku ne, mata! Lalle ne kaidinku mai girma ne! "Yusufu! Ka kau da kai daga wannan. Kuma ki nemi gafara  domin laifinki. Lalle ne ke, kin kasance daga masu kuskure." Kuma waɗansu mata a cikin Birnin suka ce, "Matar Aziz tana neman hadiminta daga kansa! Haƙiƙa, ya rufe zuciyarta da so. Lalle ne mu, muna ganin ta a cikin ɓata bayyananna".

Sa'an nan a lokacin da ta ji labari game da makircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dogara wajen cinsa, kuma ta bai wa kowace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce, "Ka fito a kansu”. To, a lokacin da suka gan shi, suka girmama shi, kuma suka yanyanke hannayensu, kuma suka ce, "Tsarki yana ga Allah! Wannan ba mutum ba ne! Wannan bai zama ba face Mala'ika ne mai daraja!" Ta ce, "To wannan ne fa wanda kuka zarge  ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙiƙa, na neme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma ni ina rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙiƙa, ana ɗaure shi. Haƙiƙa, yana kasancewa daga ƙaskantattu".

Ya ce, "Ya Ubangijina! Kurkuku ne mafi soyuwa a gare ni daga abin da suke kira na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jahilai". Sai Ubangijinsa Ya karɓa masa, saboda haka Ya karkatar da kaidinsu daga gare shi. Lalle Shi ne Mai ji, Masani. Sa'an nan kuma ya bayyana a gare su a bayan sun ga alamomin, lalle ne dai su ɗaure shi har zuwa wani lokaci.

Kuma waɗansu samari biyu suka shiga kurkuku tare da shi . Ɗayansu ya ce, "Lalle ne ni, na yi mafarkin ga ni ina matsar giya.” Kuma ɗayan ya ce, "Lalle ne ni, na yi mafarkin ga ni ina ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsaye suna ci daga gare ta. Ka ba mu labari game da fassararsu. Lalle ne mu, muna ganin ka daga masu kyautatawa". Ya ce, "Wani abinci ba zai zo muku ba wanda ake arzuta ku da shi face na ba ku labarin fassararsa, kafin ya zo muku. Wannan kuwa yana daga abin da Ubangijina Ya sanar da ni. Lalle ne ni, na bar addinin mutane waɗanda ba su yi imani da Allah ba, kuma game da Lahira, su kafirai ne. Kuma na bi addinin iyayena, Ibrahim da Is'haƙa da Yaƙuba. Ba ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kome. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutane, amma mafi yawan mutane ba su godewa. Ya abokaina biyu na kurkuku! Shin iyayen giji dabam-dabam ne mafiya alheri ko kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasawa? Ba ku bauta wa kome, baicinSa, face waɗansu sunaye waɗanda kuka ambace su, ku da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalili ba game da su. Babu hukunci face na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kowa face Shi”. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba.

"Ya abokaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shayar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, za a tsire shi, sa'an nan tsuntsaye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa." Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cewa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambace ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunawar ubangijinsa, saboda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru.

Kuma sarki ya ce. "Lalle ne, na yi mafarki , na ga shanu bakwai masu ƙiba, waɗansu bakwai ramammu, suna cin su, da zangarku bakwai kore-kore da waɗansu ƙeƙasassu. Ya ku jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkina, idan kun kasance ga mafarki kuna fassarawa". Suka ce, "Yaye-yayen mafarki ne, kuma ba mu zamo masana ga fassarar yaye-yayen mafarki ba".

Kuma wannan da ya kuɓuta daga cikinsu ya ce, a bayan ya yi tunani a lokaci mai tsawo, "Ni, ina ba ku labari game da fassararsa. Sai ku aike ni. Ya Yusufu! Ya kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shanu bakwai masu ƙiba, waɗansu bakwai ramammu suna cin su, da zangarku bakwai koraye da waɗansu ƙeƙasassu, tsammanina in koma ga mutane, tsammaninsu za su sani." Ya ce, "Kuna shuka, shekara bakwai tutur, sa'an nan abin da kuka girbe, sai ku bar shi, a cikin zanganniyarsa , sai kaɗan daga abin da kuke ci. Sa'an nan kuma waɗansu bakwai masu tsanani su zo daga bayan wancan, su cinye abin da kuka gabatar dominsu, face kaɗan daga abin da kuke adanawa. Sa'an nan kuma wata shekara ta zo daga bayan wancan, a cikinta ake yi wa mutane ruwa mai albarka, kuma a cikinta suke matsar abin sha." Kuma sarkin ya ce, ''Ku zo mini da shi." To, a lokacin da manzo ya je masa (Yusufu), ya ce, "Ka koma zuwa ga uban gidanka, sa an nan ka tambaye shi: Mene ne halin matayen nan waɗanda suka yanyanke hannayensu? Lalle ne Ubangijina ne Masani game da kaidinsu". Ya ce, "Mene ne babban al'amarinku, a lokacin da kuka nemi Yusufu daga kansa?" Suka ce, "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummunan aiki a kansa ba". Matar Aziz ta ce, "Yanzu fa gaskiya  ta bayyana. Ni ce na neme shi daga kansa. Kuma lalle ne shi, haƙiƙa, yana daga masu gaskiya. Wancan ne, domin ya san cewa lalle ne ni ban yaudaure shi ba a ɓoye, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da kaidin mayaudara. Kuma ba ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙiƙa, mai yawan umurni ne da mummunan aiki, face abin da Ubangijina Ya yi na rahama. Lalle Ubangijina Mai gafara ne, Mai jin ƙai." Kuma sarkin ya ce, "Ku zo mini da shi in keɓe shi ga kaina". To, a lokacin da Yusufu ya yi masa magana sai ya ce, "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce".  Ya ce, "Ka sanya ni a kan taskokin ƙasa. Lalle ne ni, mai tsarewa ne, kuma masani."

Kuma kamar wancan ne Muka bayar da iko ga Yusufu a cikin ƙasa yana sauka a inda duk yake so. Muna samun wanda Muke so da rahamarMu, kuma ba Mu tozartar da ladar masu kyautatawa. Kuma lalle ladar Lahira ce mafi alheri ga waɗanda suka yi imani, kuma suka kasance masu taƙawa. Kuma 'yan'uwan Yusufu suka je, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gane su, alhali kuwa su, suna masu musunsa. Kuma a lokacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce, "Ku zo mini da wani ɗan'uwa naku daga ubanku. Ba ku gani ba cewa lalle ne ni, ina cika ma'auni, kuma ni ne mafi alherin masu saukarwa? Sa’an nan idan ba ku zo mini da shi ba, to, babu awo a gare ku a wurina, kuma kada ku kasance ni." Suka ce, "Za mu neme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mu, haƙiƙa, masu aikatawa ne". Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kayansu, tsammaninsu suna gane ta idan sun juya zuwa ga mutanensu, tsammaninsu, za su komo".

To, a lokacin da suka koma zuwa ga ubansu, suka ce, "Ya babanmu! An hana mu awo, sai ka aika ɗan'uwanmu tare da mu. Za mu yi awo. Kuma lalle ne. haƙiƙa mu, masu lura da shi ne." Ya ce, "Ashe, za ni amince muku a kansa? Face dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabani, sai dai Allah ne Mafificin masu tsari, kuma Shi ne Mafi rahamar masu rahama." Kuma a lokacin da suka buɗe kayansu, suka sami hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce, "Ya babanmu! Ba mu zalunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nemo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyaye ɗan'uwanmu, kuma mu kara awon kayan raƙumi guda, wancan awo ne mai sauƙi". Ya ce, "Ba zan sake shi tare da ku ba, sai kun kawo mini alƙawarinku daga Allah, haƙiƙa, kuna dawo mini da shi, sai fa idan an kewaye ku." To, a lokacin da suka yi masa alƙawari, ya ce, "Allah ne Wakili a kan abin da muke faɗa". Kuma ya ce, "Ya ɗiyana! Kada ku shiga ta kofa guda, ku shiga ta ƙofofi dabam-dabam, kuma ba na wadatar muku kome daga Allah. Babu hukunci face daga Allah, a gare Shi na dogara, kuma a gare Shi masu dogara sai su dogara".

Kuma a lokacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yana wadatarwa ga barinsu daga Allah ba face wata buƙata ce a ran Yaƙubu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shi, haƙiƙa, ma'abucin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutane ba su sani ba. Kuma a lokacin da suka shiga wajen Yusufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce, "Lalle ni ne ɗan'uwanka, saboda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance suna aikatawa." Sa'an nan a lokacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kayan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yekuwa ya yi yekuwa, "Ya ku ayari! Lalle ne, haƙiƙa ku ɓarayi ne". Suka ce, kuma suka fuskanta zuwa gare su, "Mene ne kuke nema?" Suka ce, "Muna neman ma'aunin sarki. Kuma wanda ya zo da shi, yana da kayan raƙumi ɗaya, kuma ni ne lamuni game da shi". Suka ce, "Tallahi! Lalle ne, haƙiƙa, kun sani, ba mu zo don mu yi ɓarna a cikin ƙasa ba, kuma ba mu kasance ɓarayi ba." Suka ce, "To, mene ne sakamakonsa idan kun kasance maƙaryata?" Suka ce, "Sakamakonsa , wanda aka same shi a cikin kayansa, to, shi ne sakamakonsa, kamar wancan ne muke saka wa azzalumai".

To, sai ya fara (bincike) da jakunansu a gabanin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yusufu. Bai kasance ya kama ɗan'uwansa a cikin addinin (dokokin) sarki ba, face idan Allah Ya so. Muna ɗaukaka darajoji ga wanda Muka so, kuma a saman kowane ma'abucin ilmi akwai wani masani. Suka ce, “idan ya yi sata, to, lalle ne wani ɗan'uwansa ya taɓa yin sata a gabaninsa”. Sai Yusufu ya ɓoye  ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce. "Ku ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke sifantawa”. Suka ce, "Ya kai Azizu! Lalle ne yana da wani uba, tsoho mai daraja, saboda haka, ka kama ɗayanmu a matsayinsa. Lalle ne mu, muna ganin ka daga masu kyautatawa. Ya ce, "Allah Ya tsare mu daga mu kama wani face wanda muka sami kayanmu a wurinsa. Lalle ne mu, a lokacin nan, haƙiƙa, azzalumai ne."

Saboda haka, a lokacin da suka yanke tsammani daga gare shi, sai suka fita suna masu ganawa. Babbansu ya ce, "Shin, ba ku sani ba cewa lalle ne ubanku ya riƙi alƙawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yusufu'? Saboda haka, ba zan gushe daga ƙasar nan ba face ubana ya yi mini izini, ko kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shi ne Mafi alherin mahukunta. “Ku koma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Ya ubanmu, lalle ne ɗanka ya yi sata, kuma ba mu yi shaida ba face da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba. “Kuma ka tambayi alƙarya wadda muka kasance a cikinta, da ayari wanda muka gabato a cikinsa, kuma lalle ne, haƙiƙa, mu masu gaskiya ne." Ya ce, "A'a, zukatanku sun ƙawata wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyawo, akwai tsammanin Allah Ya zo mini da su gaba ɗaya (Yusufu da'yan'uwansa). Lalle ne Shi ne Masani, Mai hikima." Kuma ya juya daga gare su, kuma ya ce. "Ya baƙin cikina a kan Yusufu!" Kuma idanunsa suka yi fari saboda huznu sa'an nan yana ta haɗewar haushi. Suka ce, "Tallahi! Ba za ka gushe ba, kana ambaton Yusufu , har ka kasance mai rauni ƙwarai, ko kuma ka kasance daga masu halaka." Ya ce, "Abin sani kawai, ina kai ƙarar baƙin cikina da sunona zuwa ga Allah, kuma na san abin da ba ku sani ba daga Allah. Ya ɗiyana! Sai ku tafi ku nemo labarin Yusufu  da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah. Lalle ne, babu mai yanke tsammani daga rahamar Allah face mutane kafirai."

Sa'an nan a lokacin da suka shiga gare shi suka ce, "Ya kai Azizu! cuta ta shafe mu, mu da iyalinmu, kuma mun zo da wata haja maras ƙima. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yana saka wa masu yin sadaka . Ya ce, “Shin, kun  san abin da kuka aikata ga Yusufu da ɗan'uwansa a lokacin da kuke jahilai?” Suka ce, "Shin ko, lalle ne, kai ne Yusufu?" Ya ce, "Ni ne Yusufu, kuma wannan shi ne ɗan'uwana. Haƙiƙa Allah Ya yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, lalle ne Allah ba Ya tozarta ladar masu kyautatawa”. Suka ce, "Tallahi! Lalle ne haƙiƙa, Allah Ya zabe ka a kanmu, kuma lalle ne mun kasance, haƙiƙa, masu kuskure." Ya ce, "Babu zargi a kanku a yau, Allah Yana gafarta muku, kuma Shi ne Mafi rahamar masu rahama. Ku tafi da rigata wannan, sa'an nan ku jefa ta a kan fuskar mahaifina, zai koma mai gani. Kuma ku zo mini da iyalinku baki ɗaya".

Kuma, a lokacin da ayari  ya bar (Masar) ubansa ya ce, "Lalle ne, ni ina shaƙar iskar Yusufu, ba domin kuna ƙaryata ni ba." Suka ce, "Tallahi, lalle ne, kai, haƙiƙa, kana a cikin ɓatarka dadadɗa." Sa'an nan a lokacin da mai bayar da bushara ya je, sai ya jefa ta a kan fuskarsa, sai ya koma mai gani. Ya ce. "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni ina sanin abin da ba ku sani ba daga Allah?" Suka ce, "Ya ubanmu!  Ka nema mana gafara ga zunubanmu, Ialle ne mu, mun kasance masu kuskure". Ya ce, "Da sannu za ni nema muku gafara daga Ubangijina. Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai."

Sa'an nan a lokacin  da suka shiga gun Yusufu, ya tattara mahaifansa biyu a gare shi, kuma ya ce, "Ku shiga Masar in Allah Ya so, kuna amintattu. Kuma ya ɗaukaka iyayensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka faɗi a gare shi, suna masu sujada. Kuma ya ce, "Ya babana! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nawa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sosai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lokacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bayan shaiɗan ya yi fisgar ɓarna a tsakanina da tsakanin 'yan'uwana. Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shi, Shi ne Masani, Mai hikima. Ya Ubangijina, lalle ne Ka ba ni daga mulki, kuma Ka sanar da ni daga fassarar labaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincina a duniya da Lahira, Ka karɓi raina ina Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga salihai."” Ƙur’ani, sura ta 12, aya ta 4 zuwa 101.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Gumi, A. M. Alƙur’ani Mai Girma da Kuma Tarjaman Ma’anoninsa Zuwa ga Harshen Hausa. Madina: Wuri da aka tanada musamman don buga Al-Qur’ani Mai girma.

Yahaya I. Y. (1971). Tatsuniyoyi da Wasanni, Littafi Na Ɗaya. Oxford University Press.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub