Makaɗan Fada

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Fada


Gabatarwa


Ana busa algaita

Makaɗan fada su ne makaɗan da basa yiwa kowa kiɗa da waƙa sai jinin sarauta ko wanda yake riƙe da wata sarauta babba kamar irin su sarki, galadima, waziri, hakimai, dagatai, masu unguwanni da kuma irin su sarkin dogarai, da makamantansu. Waɗannan su ne asalin makaɗan fada. Amma yanzu canjin zamani ya saka irin waɗannan mawaƙa yiwa masu kuɗi da kuma masu mulki waƙa (Ɗangambo, 1984).

Makaɗan fada akan kuma kira su da makaɗan sarakuna (Zarruƙ, Kafin Hausa, da Al-Hassan, 1992). Suna yiwa sarakuna waƙa ne ba sarautar ba. Yawancin makaɗan fada suna da iyayen gidansu waɗanda su kaɗai suke yiwa waƙa, in ma sun yiwa wani, to sai sun nemi izini  a wajen iyayen gidan nasu. Su iyayen gidan nasu su suke ɗaukar dukkan ɗawainiyoyinsu na rayuwa kamawa tun daga abinci, zuwa gurin zama, zuwa sutura, da su da iyalansu.

Wata Tawagar Makaɗan Fadar Kano

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub