Makaɗan Maza

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗan Maza


Gabatarwa


Kiɗan Kokawa

Makaɗan maza su ne makaɗan da ke yiwa jarumai kiɗa da waƙa. Wato idan mutum ya yi fice a wani fage da sai jarumi ne ke yi, kamar irin su kokawa ko dambe da makamantansu, to su kuma sai su riƙa yi masa kiɗa da waƙa domin su ƙarfafa masa guiwa.

Yawancin rukunin wasanni irin su dambe, kokawa, wasa da maciji, wasa da kura, farauta, da sauran irin wasanni masu haɗari waɗanda maza zalla ke yinsu a al’adance, to waɗanda suka yi fice a wannan fage su ake yiwa wannan kiɗa.

Dubi yadda Ɗan’anace ya ke zuga Duna inda yake cewa, “…Ba a wa mutum takakka, Wandara kai ɗai ke wa mutum takakka, in ka so ka ko buge shi ka dawo…”. Wannan na daga cikin irin kalaman kurantawa da gwarzantawa da irin waɗannan makaɗa ke yiwa mazaje domin su ƙara kumbura musu kai tare kuma da ƙarfafa musu guiwa.

Kiɗan Kokawa

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan - Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub