Buzuwa Mai Sayen Takalmi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Buzuwa Mai Sayen Takalmi


Wata Buzuwa ce ta je kasuwa domin ta saya wa ɗanta takalmi. Ko da ta isa kasuwa wajen mai sayar da takalma, sai ta duba daidai ƙafar ɗan nata, ta tambayi farashi. Da mai sayar da takalma ya tashi gaya mata farashi sai ya nuna har da waɗanda suka ɗara girman ƙafar ɗan nata, ya ce da ita duk farashinsu ɗaya ne; ya gaya mata kuɗin.

Da Buzuwar nan ta ji haka, sai kawai ta ce bari ta ɗauki manyan ƙafar nan idan ta je gida sai ta rage tsayinsu da wuƙa.

Shike nan Buzuwa ta ɗauki takalma mafiya girma ta biya kuɗi ta yi tafiyarta gida. Da ta je gida, sai ta ɗauki wuƙa ta rage tsayin takalman ta gaba, sannan ta bai wa ɗan.


Labari Daga:
Sunusi Abdullahi, wanda aka fi sani da Kwamanda, Rimin Kebe, Kano. 09027362322


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub