Mahaukaci da Sallar Gawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Mahaukaci da Sallar Gawa


Wata rana wani mahaukaci ya zo wuce wa ta wani guri a wani gari, sai ya ga za ana sallatar wata gawa, saboda haka shima sai ya bi sahu. Da liman ya yi kabbarar farko a matsayin Kabbarar Harama, sai mahaukacin nan ma ya yi. Da liman ya sake kabbara ta biyu, sai mahaukacin nan ya tafi ruku'u, bayan ya ɗora hannayensa a guiwa, sai ya waiga ya ga sauran jama'a tsaye; babu wanda ya yi ruku’u sai shi kaɗai, ai kuwa mahaukacin nan sai ya ɗago ya kalli jama'a ya ce: "Shegu, sun bada ni", daga nan ya ƙara gaba abin sa; ya yi tafiyarsa.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub