Tusar Harɗo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Muƙyaƙyata: Tusar Harɗo


Wani harɗo ne ya je kasuwa, ya sayi ƙosai mai yawa da rana ya ci. Ashe ƙosan nan bai soyu sosai ba; cikinsa ɗanye-ɗanye ne. Bayan harɗo ya koma gida da daddare, sai cikinsa ya rikice.

Da dare ya yi sai harɗo ya fita gurin da suke hira tare da sauran jama’ar unguwarsa ciki kuma har da samari, ana tsaka da hira sai harɗo ya saki wata tusa mai warin gaske. Sai wani daga cikin matasan da ke zaune a wajen ya buɗe baki ya ce kaaaai, amma fa wannan tusa…, kafin ya ƙarasa faɗin abin da zai faɗa sai harɗo ya yi maza ya taka masa birki ya ce da shi kul. Saboda haka sai matashin nan ya rufe bakinsa.

Shikenan, sai aka cigaba da hira, ai kuwa da hira ta fara nisa sai harɗo ya ƙara sakin wata tusar. Da matashin nan ya sake jin tusar nan sai ya ce: “Amma fa an yi tusa mai ɗoyi”. Sai harɗo ya amsa masa da cewa: “Ba tusa ba she, iskar bazara she”. Sai saurayin nan ya sake cewa: “Gaskiya baffa idan wannan iskar bazara she to fa lallai bana za a yi ruwan kashi”.


Ana iya turo labari domin a wallafawa ta:
Was-af: 0803 964 8244 (+234803 964 8244)
Imel: rumbunilimi@gmail.com


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub