Rumbun Ilimi - Ƙa’idojin Ruba Kalma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙa'idojin Ruba Kalma


Gabatarwa

A fagen rubutun Hausa, akwai wasu ƙa’idoji da su ne ke jan ragamar mai rubutu ta hanyar nuna masa guraren da ya kamata ya raba kalmomi. Farfesa Bunza (2002), ya ce, “Wannan fage shi ne mafi faɗi da kuma rikitarwa a fagen ƙa’idojin rubutun Hausa”.

Kalma, da ita ake rubuta dukkan wani abu da ake son rubutawa. A wannan rubutu da mai karatu yake karantawa, so ake a yi bayani bakin gwargwado game da guraren da masana Harshen Hausa suka haɗu a kan cewa, wata kalmar ba ta haɗuwa da wata idan aka zo rubuta su. Ga ɗan abin da ya samu a nan ƙasa:

Kalmomi masu gaɓa ɗaiɗai

Dokar rubutun Hausa ta ce, duk kalmar da take da gaɓa ɗaya ba a raɓa ta da kowace kalma a cikin rubutu, matuƙar dai ta zo a matsayin mai cin gashin kanta. Ana samun irin waɗannan kalmomi masu gaɓa ɗaiɗai a kowane rukuni ko ajin kalmomi. Ga wasu misalai a cikin jimla:

 1. Na yi noma.
 2. Zan yi noma bana.
 3. Ya ɗora kofi a kan faranti.
 4. Za su ci abinci.
 5. Sun ci abinci.
 6. Ba na ce da kai kar ka ƙara magana da shi ba?
 7. An biya Larai bashin da ta ke bi.
 8. Hassada mugunyar cuta ce, ka yi nesa da ita.
 9. Na ji ana ihu a can.
 10. Wai an ce jan yadi ba shi da ƙarko.

Wakilin suna

Idan aka zo rubuta wakilin suna, ana kula da waɗannan ajujuwan wakilin suna; wakilin suna na farko, wakilin suna na biyu, wakilin suna na uku da kuma wakilin suna so karɓau, sai a raba su a cikin rubutu. Waɗannan ajujuwan wakilin suna, dokar rubutun Hausa ta hana a haɗe su a cikin rubutu. Ga misalai a cikin jimla:

 1. Wakilin suna na farko: Ni, da kuma mu.
  • Na yi dariya a lokacin da ya ce da mu yake magana.
  • Ni na rubuta jawabin.
  • Da mu aka ɗaura auren.
 2. Wakilin suna na biyu: Kai, ke, ku, ka ki.
  • Kai ne ka ci jarabawar.
  • Ke ya kamata ki dafa abincin.
  • Ku yi hattara wajen ɗaukar magana.
  • Ki karanta Alƙur’ani kullum.
  • Ka riƙa karanta Alƙur’ani kullum.
  •  Kin faɗi gaskiya.
  • Kun raba gardama.
 3. Wakilin suna na uku: Shi, ita, su, ya, ta, da sun.
  • Shi ya gina gidan.
  • Da shi da Ado suka zo nan.
  • Ita ta ce a baka wannan motar.
  • Su ba mutane ba ne?
  • Ka je ka gaishe su.
  • Ya zo nan ɗazu.
  • Shi ne ya cire masa haƙori.
  • Ta iya zana gida.
  • Sun saɓa ƙa’idar rubutun Hausa.
 4. Wakilin suna so karɓau: Shi ne wakilin sunan da ya karɓi aiki a cikin jimla. Misali:
  • Ya mare shi.
  • Sun jefa shi cikin rami.
  • An karya shi a ƙafa.
  • Ado ya yabe mu.
  • An raba musu littattafai.

Kalma mai zaman kanta

A dokar rubutun Hausa, duk kalmar da take cin gashin kanta a cikin rubutu ba a haɗe ta da komai. Misali:

 1. Mariya mai dafa tuwo.
 2. An ɗebo ruwa a cikin tulu daga rafi zuwa gida.
 3. Su suka rarraba kayan aikin.
 4. Ka mallaki softuwayar Rumbun Ilimi.
 5. Sai an gwada akan san na ƙwarai.
 6. Karatu abu ne mai muhimmanci.
 7. Idan ka ci ka sha, sai ka gode wa Allah.
 8. Ba ni ka ce na je garin ba.
 9. Tuwo ne a cikin kwatashin.
 10. Za ta iya yi ko da ba a ci kasuwar ba.

Harafin “a”

Idan harafin “a” ya zo a matsayin harafi mai zaman kansa a cikin rubutun Hausa, doka ta ce a rubuta shi a ware. Misali:

 1. A lokacin da Ado ya zo.
 2. Kana da rabo a lahira.
 3. A je a yi masa magana.
 4. Ka je ka sanar da alƙali a rubuce ba a magance ba.
 5. Ya ɗora littafi a kan teburi.
 6. A cikin Rumbun Ilimi na kwashi darrusa a ɓagas.

Kalmomin sharaɗi

Kalmomin sharaɗi kamar irin su idan, sai da in, dokar rubutun Hausa ta ce a rubuta su a ware. Misali:

 1. Idan ka je makaranta, za ka koyi karatu.
 2. Sai an je gidansu sannan a same shi.
 3. Ka sayo littafin rubutu in har bai haura Naira hamsin ba.
 4. Ni na san dole Ado ya je makaranta, sai dai rashin lafiya ta hana shi.

Ɗauraya:

Dokar rubutun Hausa ta ce a ware ake rubuta: Kalmomi masu gaɓa ɗaya; wakilan suna na jinsi, wakilin suna na farko, na biyu, na uku da wakilin suna so karɓau; dukkan kalmar da ta zo a matsayin mai cin gashin kanta; harafin “a”, idan ya zo a matsayin mai cin gashin kansa a cikin magana da kuma kalmomin sharaɗi.

Manazarta:

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa) Don Masu

Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adelabu Street, Surulere, Lagos-Nigeria.
Jinju M.H. (2007). Rayayyen Nahawun Hausa. Northern Nigerian Publishing Company L.T.D., Gaskiya Building, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sani M.A.Z, Muhammad A. da Rabeh B. (2000). Exams Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC,
Ibadan – Nigeria.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M. (2007). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. University Press PLC, Ibadan – Nigeria.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Uku.
University Press PLC, Ibadan-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub