Sadarwa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sadarwa A Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Sadarwa ita ce isar da saƙo tsakanin ɓangarori biyu: Mai bayar da saƙo da kuma mai karɓar saƙo ta hanyar kafar isar da saƙo wacce ka iya zama mutum ko waninsa, sannan kuma cikin sigar da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa za su iya fahimta.

Dukkan al’ummun duniya, suna da hanyoyin da suke amfani da su wajen isar da saƙonnin a tsakaninsu. Daga cikin ire-iren waɗannan hanyoyi akwai baka-da-baka, rubutu, alamu, gaɓɓai da sauransu.

A wannan rubutu da mai karatu ke karantawa, za mu yi tsokaci ne game da tsohuwar hanyar isar da saƙon Bahauhse kawai. Abin nufi, shi ne cewa rubutun zai yi magana ne kawai game da hanyar isar da saƙon Bahaushe a gargajiyance.

Hanyoyin Sadarwa

Tun dauri; wato kafin haɗuwar Bahaushe da kowace baƙuwar fuska, yana da hanyoyin da yake bi wajen sadarwa. Za mu iya dunƙule waɗannan hanyoyi zuwa:

  1. Hanyar amfani da alamomi
  2. Hanyar amfani da gaɓɓai
  3. Hanyar amfani da sauti
  4. Kayan Kiɗa
  5. Saƙon kar-ta-kwana

Manazarta:


Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa Don Masu Koyo Da Koyarwa. Ibrash Islamic Publications Centre L.T.D., 31 Adalabu Street, Surulere, Lagos.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (2011). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire Littafi na Ɗaya. University Press PLC, Ibadan, Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub