Suna a Kasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zanen Suna a Kasar Hausa


Gabatarwa

Zanen suna al’ada ce da Bahaushe ke bi yana yankawa abin haihuwa wanda ka iya zama yaro ko yarinya suna.

Farfesa Bunza (2002), ya ruwaito cewa wannan al’ada daɗaɗɗiyar al’ada ce da ta wanzu a Ƙasar Hausa tun kafin kowane sauƙaƙƙen addini. Ana yin wannan al’ada ne ta hanyar samun wasu dattawa/dattaɓai su yi zane-zane a jikin kararen rama ɓararru guda bakwai, sannan sai a ɗauka a kaiwa maijego, wanda duk ta zaɓa sai a yi amfani da zanen da ke jikinsa a raɗa wa jaririn ko jaririyar suna.

Wannan al’ada ta zanen-suna ta samu sauye-sauye da dama. Daga ciki akwai sauyin farko da ta samu yadda ya koma kawai jama’a na taruwa a ƙofar gidan da aka yi haihuwa, sai a rarraba musu goro da sauraran abubuwan da suka samu, sannan liman ya ce an sawa yaro ko yarinya suna wane ko wance. Sai kuma maroƙi ya faɗa da ƙarfi kowa ya ji. Sannan a yi addu’a, sai kuma kowa ya watse.

Su kuma yara a lokacin da ake yin wannan addu’a, sai su ruga da gudu su shiga cikin gida wajen mata su gaya musu cewa an saka wa jariri ko jaririya suna wane ko wance. A lokacin da suke gudun suna ambatar Allah ya raya wane ko wance. Duk yaron da ya yi sauri ya fara isa ya je ya sanar cewa wane ko wance aka saka, akan bashi tukuici wanda kuɗaɗe ne da alewa da goro amma ba masu yawa ba.

Sai kuma a halin yanzu da Musulunci ya yi ƙarfi, a mafiya yawan gurare musamman birane, ba a ma taruwar sai dai a raɗa sunan a masallaci.

Bikin Suna

Ta fuskacin biki kuwa, akan yi shi hawa-hawa. Akwai wanda ake yi nan-take da zarar an raɗa sunan. Akan fito da abinci jama’ar da suka taru su ci, su kuma maroƙa da makaɗa suna kaɗe-kaɗensu, an aba su abin masarufi.

Bayan kuma an gama wannan, sai su ma mata su haɗu yawanci daga karkatar rana har zuwa maraice, suna ‘yan kaɗe-kaɗe, da waƙe-waƙensu na mata, suna guɗa da sauransu. Sannan kuma sukan zo da kyaututtuka a matsayin gudunmawa ga ita mai haihuwar. Wannan taro na mata bai cika kaiwa faɗuwar rana ba.

Idan kuma haihuwar fari ce, to, akan samu mata su taru a gidan iyayen mai jego; wato gidan mata kenan, su haɗo nasu abubuwan. Bayan sun tattara abubuwan da suka tara, sai kuma su ɗauko shi da maraice zuwa gidan da aka yi haihuwa, gidan maza kenan, su zo su rarraba ga iyaye, da sauran dangin miji. Wannan rabo shi ake kira tsaraba.

Abun Lura: Akan samu saɓawar wasu abubuwa daga wani gidan zuwa wani ko kuma daga wani yankin zuwa wani yankin wanda ka iya zama ƙari ko ragi a kan abubuwan da aka zayyana a cikin wannan rubutun.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa, Yadda Yake da Yadda ake Yin sa don Masu Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publication Centre L.T.D., Suru-Lere, Lagos-Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Qananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Bukukuwa


    Wasanni



    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Kayan Kiɗan Hausa


    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub