Tatsuniya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya


Gabatarwa

Tatsuniya, ƙagaggun labarai ne na ƙarya waɗanda babu ƙanshin gaskiya a cikinsu, waɗanda Hausawa kan shirya don annashuwa da hira (Junaidu da ‘Yaraduwa, 2002).

Rabe-Raben Tatsuniya

Tatsuniya iri biyu ce:
  1. Tatsuniya ta Kacici-kacici: Ita wannan tatsuniya, tana ƙunsar tambaya ne da amsarta. Amsar tambayar, sau da yawa tana yin kama da tambayar, dangane da sauti da ma’ana (Ɗangambo, 1984).
  2. Tatsuniya mai labari: Tatsuniya mai labari ita sauraro kawai ake yi ba a ba da amsa. Misali, tatsuniyoyin da suka ƙunshi su Gizo, Ƙoƙi, Dodo, Kura, Zaki, Damo, Giwa, ‘Yar Bora da ‘Yar Mowa, da sauransu da yawa. Cikin irin waɗannan tatsuniyoyi, akan sami mutane, dabbobi da sauransu. Akan kuma nuna yadda dabbobi da dodanni ke magana ko hulɗa da mutane da sauransu.
Tatsuniya, tana da amfani. Domin a lokacin da (zamanin da ya shuɗe), lokacin da ilimi da karatu ba su samu ba a ƙasar Hausa, tatsuniyoyi da labaru, su ne makarantar ‘ya’yan Hausawa, inda suke koyon tarbiyya ko halayen kirki, hani kan miyagun halaye da kuma dabarun zaman duniya, kamar dabarun kare kai, samun abinci, da sauransu. Kuma tatsuniya, tana ba da nishaɗi da raha.

Tatsuniya ana yin ta ne da daddare. Tsofaffi da manya, sukan tara yara, suna yi musu tatsuniya, su kuma koya musu cewa, su ma yaran, su riƙa yin tatsuniya (Ɗangambo, 1984).

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M. (2003). Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub