Hausa Zaurance

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zaurance


Gabatarwa

“Zaurance zance ne, mai hankali yaka gane shi”. In ji wani mawaƙin Hausa. Shi zaurance salo ne na magana da aka

Gabatarwa

“Zaurance zance ne, mai hankali yaka gane shi”. In ji wani mawaƙin Hausa. Shi zaurance salo ne na magana da akan yi shi dan a yi ɓad-da bamin zance, ga wanda ba a son ya gane inda aka dosa. Muna ma iya kallon sa kamar wani yare ne na ɗan taƙaitaccen lokaci ake ƙirƙira a cikin Hausa, saboda gwanancewa a kan harshen Hausar. Kodayake masana harshen Hausa irin su Farfesa Ɗangambo (1984), da kuma Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992), sun tabattar da zamowar zaurance ƙirƙirarren harshe.

Abin da ya sa aka kira shi da ƙirƙirarren harshe shi cewa wasu ƙungiya ta wasu mutane waɗanda suna ma iya zama mutum biyu ko fiye, waɗanda kansu ya haɗu sosai kan tsaya su tsara salon da za su riƙa yin maganar da ba mai iya gane ta sai su kaɗai a duk gurin da suka samu kansu.

‘Yan mata su suka fi amfani da wannan salo na magana, musamman a guraren da su ke son yin wata magana ta sirri wacce ba su son kowa ya ji sai su kaɗai.

Babban darasin da wannan salo na magana ke koyarwa shi ne riƙe sirri, neman shawarar juna, haɗin kai, amincewa juna, riƙon amana, da kuma son juna.

Ana yin zaurance ne ta hanyar ƙara wasu harrufa a ƙarshen kowace gaɓa da ke cikin kalma har zuwa ƙarshen zancen. Haka nan kuma babu wata ƙa’ida da aka ajiye cewa lallai sai harafi kaza za a yi amfani da shi. A’a, su masu yin su sukan zaɓi nasu salon, saboda haka ne ma za a ga cewa waɗannan basu gane na waɗancan.

Misalin Zaurance

Jirkitacciyar magana: La ke ra ke bi ke yo ke, ta ke shi ke mu ke bar ke gu ke rin ke nan ke.

Ma'anarta: Larabiyo, tashi mu bar gurin nan.

Jirkitacciyar magana: Je ke ki ke za ke na ke bi ke yo ke ki ke, kar ke su ke ga ke ne ke.

Je ki zan biyo ki, kar su gane.

Manazarta:


Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur, Kano – Nigeria.

Junaidu I. da ‘Yar’aduwa T.M. (2003). Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub