Abdullahi Sarki Mukhtar

Me ka ke nema?


Shafin Farko


Abdullahi Sarki Mukhtar


Gabatarwa

Shi mutumin garin Kebbi ne, wacce ta zama helikwatar mulkin Jahar Kabbi. An haife shi a garin Kebbi, a ranar 21 ga watan Satumban shekarar 1949. Shi ɗa ne ga wazirin Gwandu wanda ya taɓa zama zaɓaɓɓen wakili a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya ta Legas daga shekarar 1954 zuwa 1964, sannan kuma tsohon kwamishinan ayyuka na Jahar Arewa-Maso-Yamma (North-Western State) daga shekarar 1968 zuwa 1975.

Karatu

Abubakar Ɗangiwa Umar, ya yi karatu a kwalejin gwamnati (Government College, Sokoto) ta Sakkwato daga shekarar 1964 zuwa 1968, sannan kuma ya samu nasarar shiga ‘Nigerian Defence’ daga shekarar 1969 zuwa 1972, daga nan kuma ya zarce zuwa ‘Nigerian Army Armored School, Ibadan’ a shekarar 1972, sannan ya kuma je ‘US Army Administration School, Fort Benjamin Harrison, USA’ a shekarar 1988 zuwa 1989.

Shigarsa Aikin Soja

Ya fara aikin soja a shekarar 1976 inda ya fito daga makaranta da muƙamin ‘Second Lieutenat’ a shekarar 1972.

Gogayyar Aiki

Ya riƙe muƙamai da dama a rayuwarsa ta aikin soja. Daga ciki akwai zamowarsa mai tsaron lafiyar Janaral Hassan Usman Katsina lokacin da yake ‘Deputy Chief of Staff Supreme Headquaters’, sannan kuma ya riƙe muƙamin ‘General Staff Officer in the Department of Armour, Army Headquaters’, ya riƙe muƙamin ‘Chairman of the Federal Housing Authority’ daga shekarar 1984 zuwa 1985. Abubakar Ɗangiwa Umar yana daga cikin waɗanda suka bada goyon bayan juyin mulkin da shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari.

Zamowarsa Gwamna

Lt. Colonel Abubakad Ɗangiwa Umar ya zama gwamnan jahar Kaduna a shekarar 1985, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 1988.

Barinsa Soja

Bayan barinsa wannan kujera ta gwamna, Lt. Colonel Abubakar Ɗangiwa Umar ya samu ɗaukakar matsayi zuwa Kanal (Colenel). Yana kuma daga cikin mutanen da suka yi adawa da zaɓen June 12 da shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya yi, sannan kuma sun yi yunƙurin ganin an rantsar da Marigayi M.K.O. Abiola a matsayin shugaban ƙasar Najeriya. A saboda wannan dalilin aka kama shi inda daga baya kuma aka sake shi ba tare da tuhuma a kotu ba. Bayan fitowarsa daga kurkuku sai ya yi ritaya. Saboda haka ya bar aikin soja a matsayin kanal na sojan Najeriya.

Manazarta:


Kaduna State Ministry of Budget and Planning. (2016). Kaduna State in Perspective 6th Edition. Multimate Inv. Nig. Limited, Kinkino Road, Kaduna-Nigeria.

Kaduna State Ministry of Economic Planning. (2013). Kaduna State Government, State Development Plan, 2014-2018.

Haruna M. (Ba Rana). People and Politics, a (Brief) History of Kaduna: the city of crocodiles. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gamji.com/haruna/haruna251.htm

Wikipedia (2016). Kaduna State. An ciro a shekarar (2016), daga shafin: www.wikipedia.com

Bello da Oyedele (1970).Cities of the Savannah (Babu gurin bugu).



Gwamnonin Kaduna

Masarautu


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:

       

Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub