Me ka ke nema?


Shafin Farko

Barbushe Jikan Dala


Gabatarwa

Barbushe wanda ake yiwa kirari da Barbushe jikan Dala (Dokaji 1958, Ƙwalli 1996,  Bahago 1998, da Adamu 2007), jika ne ga Maharbin da ake ganin shi ya fara zama a dutsen Dala; wanda daga sunansa aka samo sunan Dutsen. Dala yana da ‘ya’ya bakwai, babbansu shi ne Garageje. Shi kuma yana da ɗa Buzame wanda shi kuma shi ne uban Barbushe (Bahago 1998).

Dokaji (1958), da Ƙwalli (1996) sun ce Barbushe shi ne shugaba na farko da ya jagoranci jama’ar da ke zaune a sassan Kano da suka haɗa da Dutsen Dala, Fanisau, Gwauron Dutse, da Magwan. Babban dalilin da ya saka shi ya zama shugaba shi ne ƙwarewarsa wajen tsafi da harkar iskokai duk da cewa shi ƙaton mutum ne ƙaƙƙarfa kuma jarumi wanda jarumtakarsa da ƙarfinsa har sun kai yana iya kashe giwa shi kaɗai kuma ya ɗauke ta ya yi tafiya da ita har tsawon wuni guda. A wancan lokacin da ake Magana akai mai ƙarfi, ko iya tsafi shi ke zama shugaba. Sai dai shi Barbushe, ba ƙarfin ne ya sa suka zaɓe shi sai dan laƙantar hulɗa da Tsumburbura da ya yi.

A lokacin shugabancinsa ya kasance yana da wakilai daga cikin ƙabilun da ke kewaye da  wannan yanki nasa na Dutsen Dala.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Savannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub