Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Abdu Dawakin Tofa 1983 - 1983



Alhaji Abdu Dawakin Tofa

Gabatarwa

Alhaji Abdu Dawakin Tofa haifaffen garin Ƙwa ne da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta Jahar Kano. An haife shi a shekarar 1932.  

Karatu

A shekarar 1943 ya halarci makarantar Firmare ta Dawakin Tofa (Dawakin Tofa Elementary School) har zuwa 1947. Ya shiga makarantar tsakiya (Kano Middle School) ta Kano daga 1947 zuwa 1951. Ya halarci makarantar aikin gona da ke Samarun Zariya (School of Agriculture, Samaru, Zaria) daga 1952 zuwa 1954 inda ya karɓi takardar shedar karatu mai taken ‘Agricultural Assistant Certificate’ takardar da take daidai da difilomar yanzu. Ya samu babbar difiloma a fannin ‘Assistant Agricultural Supretendants’ daga makarantar aikin gona ta Samarun Zariya (School of Agriculture, Samaru, Zaria) a shekarar 1961 zuwa 1962.

A shekarar 1962, ya halarci makarantar ‘Federal Soil and Water Conservation Training Centre’ da ke Nebraska, U.S.A., ya shiga jami’ar Kansas (Kansas State University) da ke U.S.A. dan samun digiri a fannin ilimin aikin gona, inda ya fita da digiri mai taken ‘B.Sc Agricultural Education’ a shekarar 1977. Sannan kuma ya samu digiri na biyu a fannin ilimin aikin gona da faɗaɗa shi (M.Sc Agricultural Education and Eɗtension) a shekarar 1978 duk dai a wannan jami’a ta Kansas.

Gogayyar Aiki

Tun gama karatunsa na difiloma a shekarar 1954 ya fara aiki da Lardin Barno (Borno Province) inda ya riƙe muƙamin Mai taimakawa aikin gona. Shi ya riƙa kula da gwaje-gwajen amfanin gona (crop eɗperiment), noman gaurayen amfani (Miɗed farming settlements), Noman shinkafa na Jere (Jere Bowl Rice Scheme), kula da cibiyar gona ta Maiduguri (Maiduguri Farm Centre Management), da kuma kula da nazarin shuke-shuke da suka haɗa da furanni, kayan marmari da kuma kayan lambu (horticulture).
Bayan nan a shekarar 1962, ya taimaka wajen yin safiyon farko kan nagartar (preliminary survey) tsarin Kogunan Kano da Haɗeja (Kano and Haɗejia River System) ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar tallafin ƙasa-da-ƙasa da kuma ci gaba ta ‘United States’ mai suna (USAID).

Ya kuma yi aiki a matsayin jami’i mai kula da sashen aikin gona (Agricultural Division) na Gumel daga shekarar 1963 zuwa 1969. Sannan da shi aka kafa makarantar gona (farm institute) ta Ɗanzomo da ke Gumel, Panda ta Gaya, da kuma Sada da ke Kazaure. Haka nan ma cibiyar koyon aikin gona (Gwarzo Farm Training Center) ta Gwarzo.

Shi ya kafa makarantar koyon noman rani ta Kila (Kila Irrigation School). Ya zama shugaban makarantar koyon aikin gona ta Ɗambatta wacce yanzu ake kiranta da sunansa (Audu Baƙo College of Agriculture, Ɗambatta) daga 1978 zuwa 1979.

Ya zama kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun ƙasa (Commissioner for Agriculture and Natural Resources) na jahar Kano daga shekarar 1979 zuwa 1981. Daga baya ya koma kwamishinan ayyuka na musamman (commissioner for special duties). Ya riƙe wannan muƙamin na watanni uku kacal (September to November, 1981).

Mataimakin Gwamna

Majalisar jahar Kano ta wancan lokacin ta zaɓe shi ya zama mataimakin gwamnan Kano a ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 1981 (24 November, 1981).

Zamowarsa gwamnan Kano

Ya riƙe wancan muƙami na Mataimakin Gwamna har zuwa watan Mayu na shekarar 1983 (May 1983) inda aka naɗa shi gwamnan Kano bayan barin kujerar da marigayi gwamna Rimi ya yi dan tsayawa takara a zaɓe na gaba. Ya riƙe wannan kujera ta gwamna tsawon watanni bakwai.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Danyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taxation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Yakasai T. (2004). Tank Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nig


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub