Gwamna Malam Ibrahim Shekarau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau 2003 - 2011



Gwamna Shekarau.

Gabatarwa

Malam Ibrahim Shekarau, dandaƙaƙƙen malamin makaranta; masanin fannin karantarwa da harkar ilimi; gogaggen ma’aikacin gwamnati; fitaccen ɗansiyasa, sannan kuma basarake mai riƙe da sarautar Sardaunan Kano. Mutum ne shi mai haƙuri, sauƙin hali, kirki da kuma biyayya ga duk wanda ke gaba da shi, a shekaru ko kuma a mulki.  

Ya karanci fannin lissafi, ya kuma karantar. Daga malamin aji ya fara, har sai da ya zama babban ministan ilimin Najeriya, duk bisa cancanta.  Saboda haka shi tsohon gwamnan Kano ne, sannan kuma tsohon ministan ilimi na tarayyar Najeriya, kuma ɗantakarar shugaban ƙasa a tarayyar Najeriya.

Haihuwa

An haifi malam Ibrahim Shekarau a unguwar Kurmawa da ke cikin birnin jahar Kano, a ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 1955. Mahaifinsa tsohon ma’aikacin Hukumar Gargajiya ne a matsayin ɗandoka, wanda ya yi aiki tare da sarkin Kano mai rasuwa; Alhaji (Dr.) Ado Bayero.

Karatu

  1. 1961 – 1967: Makarantar Firamare ta Gidan Makama.
  2. 1967 – 1973: Makarantar Sikandire ta Malam Aminu Kano, Goron Dutse, Kano (Aminu Kano Commercial College, Kano).
  3. 1973 – 1977: Jami’ar Ahmadu Bello Zaria. Inda ya yi karatun digiri a fannin ilimi da lissafi (Degree in Mathematics Education).

Gogayyar Aiki

Malam Ibrahim Shekarau gogaggen ma’aikaci ne a fannin ilimi, wanda ya fara tun daga malamin aji har sai da ya zama sakataren dindin (Permanent Secretary) a jahar Kano.

  1. 1978 – 1979: Malamin Lissafi a Kwalejin Kimiyya ta Wudil (Government Technical College, Wudil).
  2. 1979 – 1993: Shugaban makarantu (Principal) na makaratu kamar haka; ya fara da Ƙaramar Sikandire ta Wudil (Principal Government Day Junior Secondary School, Wudil); Sinkandiren gwamnati ta Haɗejia (Government Secondary School, Haɗejia); Kwalejin gwamnati ta Birnin-Kudu (Government College, Birnin-Kudu); Sikandire gwamnati ta Gwammaja (Government Secondary School, Gwammaja); daga ƙarshe kuma Kwalejin Rumfa ta Kano (Rumfa College, Kano).
  3. 1993 – 1995: Ya riƙe muƙamai a ma’aikatar ilimi ta jahar Kano kamar haka: Muƙaddashin Daraktan Ilimi na  yankin Bichi (Deputy Director of Education, Bichi Zonal Education Area); Daraktan Tsare-Tsare, Nazari, da kuma Ƙididdiga na ma’aikatar Ilimi ta Jahar Kano (Director Planning, Research and Statistics, Ministry of Education, Kano); Sakataren dindin na Ma’aikatar Ilimi da Cigaban Matasa (Permanent Secretary, Ministry of Education and Youth Development, Kano).
  4. 1995 – 1997: Sakataren dindin na ma’aikatar albarkatun ruwa, da kuma haɓɓaka karkara da birane (Ministry of Water Resources, Rural and Community Development).
  5. 1979 – 2000: Sakataren dindin na ma’aikatar Ilimi (Ministry of Education). Bai kai shekara ɗaya a wannan ma’aikata ba aka mayar da shi ofishin sakataren gwamnatin jaha fannin kula da dukkan ayyuka (General Service Directorate of the Cabinet Office).
  6. 2000 – 2001: Malamin lissafi a babbar makarantar share fagen shiga jami’a (CASRS), da ke Kano.

Ritaya

Malam Ibrahim Shekarau ya bar aikin gwamnati a ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 2001. Daga nan kuma ya zama sakataren fitaccen ɗankasuwar nan Alhaji Aminu Ɗantata.

Siyasa

Malam Ibrahim Shekarau ya shiga jama’iyyar siyasa ta ANPP a shekarar 2003.
Gwamna

Da shigarsa siyasa, malam Ibrahim Shekarau ya tsaya takarar gwamnan jahar Kano a ƙarƙashin tutar jama’iyyar ANPP, a shekarar 2003. Ya yi nasarar lashe wannan zaɓe da aka gudanar a wannan shekarar inda ya gaji gwamna mai barin gado; Injiniya (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sannan kuma ya sake lashe zaɓen da aka gudanar a karo na biyu a shekarar 2007. Abin da ya bashi damar kafa tarihin gwamna da ya fara cin zaɓe a karo na biyu a jere a tarihin jahar Kano tun da aka kafa ta a shekarar 1967.

Gudunmawa

Malam Ibrahim Shekarau, a matsayinsa na wanda ya riƙe jagoranci jahar Kano a matsayin gwamna na tsawo shekaru takwas ya bayar da gagarumar gudunmawa. Fitattu daga cikin irin abubuwan da ya yi akwai:

  1. Kafa Hukumar Adaidaita Sahu: Hukumar da ta riƙa tsaftacce tarbiyyar jama’ar jahar Kano. Daga cikin abubuwan ambato da wannan hukuma ta bari akwai samar da babur mai ƙafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep amma a Kano ake kiran sa da Adaidaita Sahu har yau ɗin nan (2017).
  2. Ya yi manya da ƙanan titunan da suka riƙa harhaɗa tsakanin karkaru da dama.
  3. Kafa Hukumar walwala da jin daɗin alhazai ta kano (Hajj Commission).
  4. Inganta Shari’ar Musulunci.
  5. Kafa Hukumar Yaƙi da Rashawa.
  6. Kafa Hukumar Hisba.
  7. Ciyar da Abicin Kyauta a Lokacin Azumi.
  8. Kafa Asibitin Gingiyu da na Titin Gidan Zu.
  9. Gina sababbin makarantun firmare da sikandire.
  10.  Hana karɓar kati a asibiti.
  11.  Rabawa malaman manyan makaratun (Lecturers) kwamfuta kyauta dan gudanar da nazari.
  12.  Kafa sabuwar ma’aikatar mata (Ministry of Women Affairs and Social Welfare).

Sarauta

An yi wa malam Ibrahim Shekarau sarautar Sardaunan Kano a zamanin sarkin Kano marigayi, Alhaji (Dr.) Ado Bayero. Sarautar da shi ne mutum na farko da aka fara yiwa ita a faɗin masarautar ta Kano tun da aka kafa ta a shekarar 999. Sannan kuma shi ya ke riƙe da wannan sarauta har zuwa yau ɗin nan (2017).

Takarar Shugabancin Ƙasa

A ƙarshen ƙarewar wa’adin mulkinsa a karo na biyu a matsayin gwamnan jahar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya yi takarar shugabancin Najeriya a kakar yaƙin neman zaɓe da aka yi a shekarar 2007.

Ministan Ilimi

Shugaban ƙasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya naɗa Malam Ibrahim Shekarau babban ministan Ilimi na Najeriya. Muƙamin da ya riƙe daga shekarar 2013 zuwa 2015.

Manazarta


BBC Hausa (2011). Takaitaccen tarihin Malam Ibrahim Shekarau. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://www.bbc.com/hausa/news

Kano Y. I. (2015). Where is Malam Shekarau? Jaridar Daily Trust ta ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 2015. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: https://www.dalytrust.com.ng

Saraj (2010). Shekarau @ 55 years and Achieɓements in Kano. an ciro a shekarar 2017, daga shafin: https://economicconfidential.com/

Wikipedia (2017). Ibrahim Shekarau. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: https://en.m.wikipedia.org

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003.

Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub