Shafin Farko

Kasuwar Dawanau, KanoWani Yanki Na Kasuwar Dawanau


Gabatarwa

Wannan kasuwa ta Dawanau, kasuwa ce ta ƙasa-da-ƙasa wacce take a garinKan. An kafa wannan kasuwa ta Dawanau a shekarar 1985. Wannan kasuwa an samar da ita ne da nufin rage cunkoso aKasuwar Sabon Gari. Wannan kasuwa katafariyar kasuwa ce ta kayan amfanin gona, wacce aka haƙƙaƙe cewa ita ce kasuwar kayayyakin amfanin gona mafi girma a duk faɗin Afirka ta Yamma (dtMaize, 2015; CNBC, 2014; International Livestock Research Institute, 2004; Aminu, 2014; Adebayo, 2016).

Haja

Ana sayar da dukkan nau'ukan kayan amfani gona. Amma an fitar da Zoɓorodo, riɗi, ƙaro, citta, 'ya'yan tafasa, zogalai, doya, busasshiyar rogo, nau'ukan hatsi (Gero, dawa, maiwa da sauransu), barkono tsidugu, tsamiya, kuka, da sauransu.

Abokan Hulxa

Zamowar wannan kasuwa babbar kasuwar duniya tana hulɗa da ƙasashen da suka haɗa da Amurka, Jamani, Daular Larabawa (Dubai), Ingila, Saudi Arabia, Indiya, Nijar, Togo, Jamhuriyar Binin (Kwatano), Kamaru, Chadi, Ghana, Burkina Faso, Afirka ta Tsakiya (Central Afrique), Laberiya, Mali, Libiya da sauransu.


Mota Tana Lodin Zoɓo Rodo Zuwa Ghana

Manazarta:


Adebayi I. (2016). Dawanau: The Story of Africa's Largest Grain Market. An ciro daga: http://www.dailytrust.com.ng/news/weekend-mag/dawanau-the-story-of-africa-s-largest-grain-market/141693.html#60muLKXtLmQOmYfZ.99. A shekarar 2016.

dtMaize (2015). Dawanau Market in Kano Nigerian Market Info Series.http://dtmaize.blogspot.com.ng/

Nigerian Trade Info Portal (2010). Exporting Yam Tubers ( Yam Tubers Product Profiles ). http://www.tradeinfong.com/2010_05_01_archive.html

CNBC (2014). Will African investments pay off?: http://www.cnbc.com/2014/06/17/will-african-investments-pay-off.html

International Livestock Research Institute (2004). Annual Report, 2004. An ciro daga: https://books.google.com.ng/books. A shekarar 2016.

Aminu A.K. (2014). Nigeria braced for potential food crisis as forecasters predict short rainy season. The Guardian Newspaper. An ciro daga: http://www.theguardian.com/global-development/2014/mar/26/nigeria-food-crisis-short-rainy-season. A shekarar 2016.

Tattaunawa da Ibrahim Muhammad Muhammad jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar kasuwar Dawanau a ranar 27/12/2018 a Kasuwar Dawanau.