Shafin Farko

Kasuwar Ƙofar Wambai


Gabatarwa

An gina wannan kasuwa ta Ƙofar Wambai a Daf da wannan Ƙofa ta Wambai. An gina ta 1977. Dalilin gina ta shi ne sauƙaƙa cunkoson da ke akwai na Kasuwar Kantin Kwari. Wannan kasuwa tana da fasali irin na zamani. Rumfunanta na zamani ne kuma sannan tana da manyan layuka da motoci ke iya ratsawa da rana alhali kasuwa tana tsaka da ci.


Wani layi a cikin Kasuwar Ƙofar Wambai, Kano.

Wannan kasuwa ta shahara da kayayyakin sutura kamar irin su gwanjo da kuma yadudduka. Sannan kuma da takalma da jakakkuna irin na mata. Ana yin takalma, riguna, da kuma jakakkuna a wannan kasuwa.

Sannan kuma wani abin sha’awa shi ne cewa wannan kasuwa fa yanzu ta haɗe da Kasuwar Kantin Kwari. Tun daga tsallaken kasuwa daga Kudu da kuma Yamma na kan titin IBB, duk shaguna ne da masu rumfuna har zuwa Kasuwar Kantin Kwari.

Wannan kasuwa tana nan a cikin ƙwaryar birnin Kano. Arewa da ita babban masallacin idin Kano ne, titi ne ya rabasu. Yamma da ita kuma unguwar Ƙofar Wambai ce zuwa Zango. Sai Arewa da ita kuma kawai unguwar malafa, layi ne ya raba tsakaninsu. Ta Gabas kuma akwai Unguwar Fagge, wacce titin IBB ya shiga tsakaninsu.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jallabar Hausa.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.