Shafin Farko

Kasuwar Kantin Kwari, Kano



Wani Yanki Na Kasuwar Kantin Kwari


Gabatarwa

Kasuwar Kantin Kwari tana daga ciki daɗaɗɗu kuma kasuwannin ƙasa-da-ƙasa a cikin garinKanoa TarayyarNajeriya.

An kafa wannan kasuwa a cikin shekarar 1934. Sunan wannan kasuwar ya samo asali ne daga wani kwari mai suna Kwarin Gogau. Har yanzu akwai ɗan sauran zirin wannan kwari a cikin Fagge. Ita kuwa wannan Unguwa ta Fagge tana daga tsallaken wannan kasuwa ta Arewa. Titi ne kawai ya raba wannan kasuwa da wannan Unguwa. Kuma kusan a yanzu ma ana iya cewa sun haɗe sun zama abu guda. Saboda idan ka tsallako daga wannan kasuwar, to layin Farko na Unguwar ta Fagge daga Kudu da ita Kasuwar Kantin Kwari, idan aka tsallake titi kenan; wato Arewacin Unguwar ta Fagge, Duk shaguna ne. Misali, a ɗauka tun daga bakin silimar Filaza a runtuma Arewa har zuwa mahaɗar Kwanar Singa, duk shagunan kasuwa ne.

Alhaji Alasan Ɗantata, da Mamman Goda suna daga sahun mutanen farko waɗanda suka fara gina rumfuna a wannan kasuwa. Daga baya Ƙwarori suka zo sannan kuma sai Larabawa. Har yanzu akwai Ƙwarori a wannan kasuwa. Idan ka shiga ‘Unity Road’ da ke kasuwar kusan Kantunan su Ƙwarorin ne da kuma gidajensu a haɗe. Saboda kasantuwar su baƙi, sai suka riƙa gina bene, ƙasa kasuwa, sama kuma gidan kwana da iyalansu. Kuma har yanzu akwai sauran wannan tsarin.

Wannan kasuwa ta Kantin Kwari tana daga cikin manyan kasuwannin Kano, akwai tarin dukiya a wannan kasuwa. Cike take maƙil da sutura.

Haja

Babbar hajar da ake kasawa a wannan kasuwa ita ce sutura kamara tun daga kan yaduka, shadda, atamfofi, leshi-leshi, gyalalluka, da sauran su


Wani Yanki Na Kasuwar Kantin Kwari

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Executive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.