Shafin Farko

Kasuwar Rimi


Gabatarwa

An gina wannan kasuwa a shekarar 1937. Sunan wannan kasuwa ya samo asali ne daga bishiyar da aka fara yin kasuwar a gidinta. Asalin wannan kasuwa akwai ta tun can baya zamanin wani sarki da ya zama matansa, ‘ya’yansa da bayinsa suna zuwa su yi cefane. Saboda haka ne ma wasu lokutan akan kira ta da kasuwar dole ko kasuwar Laraba.

Wannan kasuwa ta taskace kusan dukkan wani nau’i na abinci. Ana samun abincin gargajiya da na zamani. A wannan kasuwa ake samun kayayyaki kamar irin su zogale, rama, albasa, kanwa, daddawa, gero, da sauransu.

Sannan kuma a yanzu ana samun kusan dukkan kayan ƙyale-ƙyale da kayan ƙarau na mata, waɗanda suka haɗa da na gyaran ɗaki da kuma gyaran jiki. Ana samun kayayyaki kamar irin su ɗankunnen gwal, kayan yari, da sauransu. Haka nan ta ɓangaren kayan ɗaki akwai kaya irin su rose, samiru, da sauransu. Sannan kuma har yau ɗin nan mata su suka fi cin wannan kasuwa.

Manazarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.