Shafin Farko

Kasuwar Sabon Gari


Gabatarwa

An gina wannan kasuwa ta Sabon Gari 1914, amma bata kankama ba sai a cikin 1915. Ita kuma wannan kasuwa unguwar Sabon Gari ce ta samar da ita. A lokacin da aka haɗe lardunan Arewa, Kudu, da kuma Legas su ka zama abu guda, sai ya zama jama’ar Kudancin Najeriya sun taso zuwa garuruwan Arewa. To da yake akwai bambamcin al’adu da kuma addinai, sai ya zama a wancan lokacin cakuɗuwar waɗannan baƙi da kuma asalin ‘yan ƙasa ya yi wahala. A saboda haka sai aka tsugunnar da su a wannan yanki. To sai ya zama suna gudanar da ‘yar cinikayyarsu a guraren da suke. Da haka kasuwar Sabon Gari ta samu.


Wani yanki na shagunan kayan laturonik a cikin Kasuwar Sabon Gari

An sake ginata a ƙarƙashin gwamnatin Kano da gini irin na zamani a shekarar 1983. Aka gina mata rumfuna da janbulo. Wanda a wannan zamani shi ne ƙarshe wajen gini. Wannan kasuwa ita ce babbar kasuwar Kano. Ana samun dukkan wasu nau’ukan kayan masarufi, tufafi, suturu, musamman na Turawa, takalma, magunguna na Bature, da sauransu.


Wani yanki na shagunan kayan Sutura a cikin Kasuwar Sabon Gari

Manzarta:


Barau A.S. (2007). The Great Attractions of Kano. Research and Documentation Directorate, Office of the Eɗecutive Governor, Government House, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ɗanyaro M.M. (1997). Kano State 30 Years of Statehood (1967 – 1997).

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Gwadabe M.M. (2008). Land, Labour and Taɗation in Kano Native Authority: the Case of Kumbotso District 1903-1953. History Department, Ahmadu Bello University, Zaria.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.

Kano State Ministry of Commerce. (2000). Kano State of Nigeria, Centre of Commerce. An buga a Sagagi Press, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Obii-Mbta R.A. (1994). Alhaji Ado Bayero and the Rorayl Court of Kano. Carpricorn 25 Limited. Kano-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.