Shafin Farko

Tarihin Masarautar Kano


Gabatarwa

Kano gari ne mai daɗaɗɗen tarihi. Akwai ra’ayuyyuka mabambanta dangane da asalin wanda ya kafa garin Kano, da kuma ƙarnin da aka kafa ta. Amma zance mafi shahara shi ne cewa an kafa Kano ne a ƙarni na tara (Dokaji 1958; Ashiwaju, Enem, da Abalogu, babu shekarar bugu).

Dangane da mutanen da suka kafa garin Kano, Dokaji (1958), ya tafi akan cewa wasu maharba waɗanda ba a san ko su wanene ba, kuma ba a tabbatar daga ina suka fito ba, sai dai cewa ana ganin daga arewaci suka zo yankin da nufin farauta, su suka fara zama a wannan yankin.

Daga cikin irin waɗannan mutane akwai wanda ake ganin shi ya fara zama a wani dutse da daga baya aka riƙa kiran dutsen da sunansa. Sunan wannan mutumin shi ne Dala. Saboda haka sai aka riƙa kiran dutsen da "Dutsen Dala". Shi kuma Dalan nan mutum ne mafaruci kuma yana da 'ya'ya.


Dutsen Dala. An samo wannan hoto daga shafin: https://www.flickr.com/photos/whereiseggy/252481258. A shekarar (2016).

Shi Dala, da jama'arsa suna zaune a wannan Dutse na Dala wanda yanzu ya zama babbar unguwa, kuma ma aka samu ƙaramar hukuma guda "Dala" a jahar Kano wacce ke da helikwata a Gwamaja. Sannan kuma akwai wasu mutanen da suma suke zaune a kan Gwauron Dutse, wasu kuma a dutsen Fanisau, wasu kuma a Magwan, wasu kuma suna zaune a Tanagar (Dokaji, 1958; Ƙwalli, 1996; Adamu, 2007), duk sun tafi akan wannan.


Gwauron Dutse

Waɗannan jama’a sun riƙa kai-komo tsakankanin waɗancan duwatsu da aka ambata da kuma wani kurmi da ke kusa da gurin suna aikinsu na farauta. Wannan kurmi daga shi aka samo sunan kasuwar kurmi, sannan kuma shi ne ya haifar da kogin jakara. Waɗannan mafarauta da tafiya-ta-yi-tafiya sai suka fara jarraba noma a wannan yankin kurmin. Da suka gwada kuma sai suka yi dacen cewa wannan ɗasa tana da albarka. Saboda haka sai suka riɗa yin farauta sannan kuma suna noma.

Amma Bahago (1998), ya kawo a littafinsa cewa wani mutum da ake kira Dala, shi ya fara zama a kan Dutsen Dala shi da matansa wanda daga baya suka haifi ‘ya’ya har guda bakwai. Wannan mutum an ce daga arewa ya fito.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Ashiwaju G., Enem U. da Abalogu U. (babu shekarar bugu). Cities of the Savannah, A History of Towns and Cities of the Nigerian Savannah. By Nigerian Magazine.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Emenari R. da Barde I. (1994). Kano 100 Politics and Business. Printed at RAI Communications 10A, Galadima Road, Sabon Gari, Kano.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

William-Mbta L. A. O. (2001). The Four King-Makers, King-Making in Kano Kingdom. Published in Nigeria by Capricon, 25 Limited, Kano.